A wannan makon mun kawo muku karashen hirra da wakiliyarmu ta yi da Fitacciyar Jarumar fina-finan hausa da ke masana’antar Kannywood HADIZA MUHAMMAD wadda aka fi sani da HADIZA KABARA, ta bayyana irin kalubalen da suka fuskanta sama da shekara ashirin kafin shigarsu cikin masana’antar Kannywood, har ma da bayan shigar su, ta kuma yi bayani dangane da wasu abubuwan da suka shafi rayuwarta da kuma sana’arta ta fim.
Ga dai tattaunawar tare da wakiliyar tamu RABI’AT SIDI BALA kamar haka;
- ’Yar Kasuwa Elizabeth Homes: Labarin Tashe Da Rushewarta (I)
- Dole A Hada Karfi Wajen Dakile Bazuwar Makamai A Afirka –Buhari
Daga cikin fina-finan da kika yi wanne kika fi so, wanda ya zama shi ne bakandamiyarki, kuma me ya sa kike son shi?
Duk wani fim da kika ganni a ciki ina son shi ne na yi, domin da bana son shi ba yadda ma zan karbi aiki na yi, ba fim din da bana so, ba ni da wani bakandamiya ko na fi son wannan ko wancen, dukka fim da kika ga na fito a ciki ina son shi nayi shi, ba wai bana son shi nayi ba, in bana so ma ba zan ma karbi aikin ba, ba zan ma taka rawar ba.
Ko kina da ubangida ko iyayen gida a cikin masana’antar Kannywood?
Sosai ma kuwa ina da ubangida, za ka yi harkar fim ne ka ce ba ka da ubangida?, ni ko nake da ubangida sosai ma, ba iyayen gida ba, maigidana daya ne kwal.
Ko za ki iya fadawa masu karatu sunansa?
Ubangidana kowa ya sani dai, Falalu A.Dorayi shi ne ubangidana a yanzu, ba ni da wanda ya fi shi.
Ya batun nasarori, wanne irin nasara kika samu game da fim?
An samu nasarori sosai wanda ba za su misaltu ba sai dai Alhamdulillah, amma shi ma sirri ne ba zai fadu ba, Alhamdulillah, Allah ya karawa Annai daraja (S.A.W).
Mene ne gaskiyar maganar jita-jitan da ke yawo na za ki auri Nabariska?
Wannan maganar ba ni da amsarta, don Allah ki ajjiyeta, ki dauko wata maganar me mahimmanci mu yi dan Allah.
Ya kika dauki sana’ar fim a wajenki?
Na dauki sana’ar fim sana’a ingantacciya wadda ba irinta tunda ni sana’a ta ce, kin san kowa da sana’arsa yake tutiya, na dauke ta da daraja da mahimmanci. Sannan kuma ni din nan da kike gani ban taba dana sanin shiga fim ba, sabida anan abinci na yake, anan kaddarata take a rayuwata ta duniya. Toh! kullum ina rokon Allah, Allah ya kara dafa mun, ko kuma na ce Allah ya dafa mana baki daya. Amma tunda nake ban taba dana sani ba, ta samun kaina a harkar fim kaddarata kenan a rayuwa, ban taba jin wani abu ba, alfahari ma nake da harkar, in ka gannu ma in baka ce mun ‘yar fim ba kai ka sani, wannan ya rage naka, amma ni ina alfahari da fim.
Wanne buri kike son cimma?
Wallahi harkar fim na cimma abubuwa da yawa, sosai ma.
Mene ne burinki na gaba game da harkar fim?
Babban burina kawai na ga harkar fim din tafi haka ma, na ga harkar fim din ta mamaye ko ina, sana’a ce me daraja, burina a rayuwa Allah ya sa mu gama lafiya.
Bayan sana’ar fim, kina wata sana’ar ne?
Ina da sana’ar da nake sana’a dai haka ta mata, a je a saro kaya a siyar, yanzu ne ma kin san yanayin hanya ba dadi, ina zuwa har kwatono, Legas, na je na siyo kaya na zo na siyar. Nan ma kwari na je na siya, yanzu ne na fi karfi na je kwari na dan tsittsinta abin da nake so, na zo na siyar.
Ya alakarki take da sauran Jarumai?
Alakata da kowanne jarumi walau mace walau namiji lafiya kalau, indai a masana’anta yake to muna nan lafiya kalau, ba ni da matsala da kowa da yardar Allah, kowa nawa ne.
Wace ce babbar kawarki a kannywood?
Kawayena suna da yawa ba zan ce ga wance ba, ga wance ba, ina da babbar kawa a Kannywood, duk matar da take a kannywood ai kawata ce.
Wanne abu ne ya taba faruwa da ke na farin ciki ko akasin haka wanda ba za ki taba mantawa da shi ba?
Abubuwa da yawa sun faru da ni na farin ciki, na bakin ciki ma sun faru da ni ba za su fadu bane kawai na barwa Allah, kuma n barwa raina. Bari na baki misali guda daya, akwai lokacin da wayata ta fadi, muka je wani aiki Katsina, Ali Nuhu ya ga wata ‘yar karamar waya a hannuna ya ce “Hadiza ya ya haka, waya karama a hannunki?, ana ta tuttura abubuwa social media ba a ji kin yi magana ba”, sai na ce “ai an sace mun waya, wayata faduwa ta yi wallahi an dauke mun waya, ba ni da waya’. Sai ya ce “Toh! ba komai inshaAllahu muna komawa ki tuna mun”, na ce to. Da kamar ba zan tuna masa ba, ina dan tunanin ba zan takura masa ba, na dai yi karfin hali dai na tambaye shi. Wallahi cikin ikon Allah ya saya mun waya sabuwar dal ya bani, a kwali da komi da komai, har yana ban hakuri ma. Wannan abin ya matukar faranta mun rai, ya yi girma a raina sosai, ba abin da zan ce sai godiya. Yanzu kamar dan uwana shi kansa Falalu Dorayi abubuwan faranta mun da ya yi suna da yawa, wani abun ma ba za su fadu ba wallahi, kin san mutum in ya yi maka abu zai maka dan Allah ne ba dan ka zo ka fada ba, amma akwai ire-irensu da su ka yi mun abubuwa da yawa da ba za su misaltu ba, ko kuma iri-irensu da sukai mun abu uwa da yawa da suka bata mun rai, wanda kawai ma bana son na tuna bare na fada.
Wanne irin abinci da abin sha kika fi so?
Ina son shinkafa da miya da salad, da naman rago. Abin sha kuma na fi son ruwa.
Wanne kira za ki yi ga masu kokarin shiga masana’antar Kannywood har ma da wadanda suke ciki?
Wanda suke kokarin su samu su shigo, su ahigo da wankakkiyar zuciya, in sana’ar ka zo yi, ubangiji zai daf maka, sy zo tsakaninsu da Allah da zuciya daya. Idan suka zo zuciyarsu daya tsakaninsu da Allah ba wani abu a ransu ko wani rashin ji, ko wani abu, da yardar Allah zai dafa musu. Amma da iyayensu da ‘yan uwansu. Wanda suke cuji kuma allah ya ci gaba da hada .
Wanne irin kaya kika fi son sakawa, kuma wanne kala?
Na fi son na saka atampa kowacce iri na fi son na saka ta ko leshi, ko wanne kala ina so.
Ko akwai wani kira da za ki ga gwamnati game da harkar fim?
Kiran da zan yi ga gwamantin Kano ba abin da zan ce sai dai na ce dan Allah ta kara mana kaimi, ta sa mana hannu harkar mu ta tafi dai-dai.
Me za ki ce da makaranta wannan shafi na RUMBUN NISHADI, da ita kanta gidan Jaridar LEEADERSHIP HAUSA?
Ba abin da zance da wannan gidan jarida me tarin albarka wato LEADERSHIP, na san ina jinta tun ina karama ba tun yanzu ba, toh Allah ya kara mata daukaka, abin da zan ce kenan, kuma ina yi mata fatan alkhairi Allah ya sa tafi haka, alfarmar sayyiduna rasulullah (S.A.W). Masu karatu ina yi muku fatan alkhairi, dan Allah a taya mu da addu’a mu yi lafiya mu gama lafiya, ina yi wa kowa fatan alkhairi da iznin Allah.
Ko kina da wadanda za ki gaisar?
Ina gaida kowa da kowa na fadin Nijeriya gaba daya, musamman musulman mu, ina yi wa kowa fatan alkhairi, dama wanda ba musulman ba wanda suke kallon rubutun mu.
Muna godiya
Ni ma na gode