Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, ya yi matukar yabawa da jajircewar mataimakinsa, Sanata Kashim Shettima, wanda ya bayyana shi a matsayin mutum mai amana da kuma gaskiya da yake jin dadin yin aiki da shi.
A wata sanarwa da shugaban kasar ya fitar, don taya mataimakin nasa murnar cika 59 a duniya, Tinubu ya bayyana cewa; “Tun daga lokacin da na san ka zuwa yanzu, ba ka taba nuna gajiyawa wajen yin aiki tukuru ba, musamman domin sake gina wannan kasa tamu.
- Sulhu Da ‘Yan Bindiga Ya Fara Haifar Da Da Mai Ido A Katsina
- Kowa Ya Ci Zomo Ya Ci Gudu: Shekaru 80 Da Nasarar Sinawa A Kan Zalunci Da Danniyar Japanawa
A dukkanin mukaman da ka rike a baya, ka nuna jajircewa wajen aiwatar da abubuwan da suka dace, duk runtsi duk wahala,” in ji shugaban kasar.
Tinubu ya kara da cewa, yana matukar godiya bisa irin goyon bayan da yake samu daga wurin Shettima, “lokacin da na zabe ka a matsayin mataimakina, na san ko alama ban yi zaben tumun-dare ba, domin kuwa na san na dauko nagartacce mutum, wanda Nijeriya za ta yi alfahari da shi. Kullum a aikinka na mataimaki, kana kokari wajen kawo shawarwari daban-daban tare da tsara sabbin abubuwan da za su taimaka mana wajen sauke nauyin da muka dauka.”
“Ban yi da-na-sani, wajen zabenka a matsayin mataimaki. Tare da kai muka fara aikin dawo da martabar Nijeriya ta hanyar gyare-gyare da matakan da muka fara dabbakawa a shirinmu na ‘Renewed Hope Agenda’,” in ji shi, sannan ya kara da cewa; alakarsu ta wuce iya maganar aiki kadai.
Har ila yau, Tinubu ya bayyana cewa; suna matukar samun nasarori da dama tare, “Ka sake nuna mana irin nasarorin da za a samu, idan aka sadaukar da kai tare da hadin kai; wajen ciyar da kasa gaba, wanda hakan shi ne abin da ya kama masu zama shugabanni su koya.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp