Shugaban kungiyar manoman masara don samun riba na yankin Arewa maso gabas Alhaji Adamu Muhammad Makarfi, ya sanar da cewa, a bana, an yi noman masara da tsadar gaske, saboda tashin farashin takin zamani, inda kudin buhu daya ya kai kusan naira 30,000.
Adamu a hirarsa da LEADERSHIP Hausa a kaduna ya ce, sabin yadda ake sayar da takin kan naira 5,000 a baya, a bana farashinsa ya ninka, inda ya ce, hatta magungunan feshi na kwari ko na kashe ciyawa da kudin kwadago, sun karu.
- Yayin Da Yakin Neman Zaben 2023 Ya Kankama…
- Kiraye-Kirayen Neman Gwamnatin Tarayya Ta Karbi Wasu Filayen Jiragen Sama Na Jihohi
Ya ci gaba da cewa, haka ambaliyar ruwan sama da aka samu a wasu jihohin kasar nan kamar su Zamfara da Sakkwato da Jigawa da Katsina da kaduna da wasu jihohin duk an samu wannan iftila’in, inda hakan ya jawo wa manoma yin asara.
Ya kara da cewa, “A matsayina, na manomi mu bukatar mu ba wai a sayar da amfanin gona da tsada a kasar nan ba, amma duk da haka, ba za mu so ace manoma sun yi asara ba, domin asarar manoma, asara ce ga kasa baki daya”.
Ya yi nuni da cewa, domin duk inda aka ce manomi ya yi noma kuma ya fadi, babban abin da ake jin tsaro, musamman manyan manoma da yawancin su suke yi don riba in sun fadi akwai matsala domin akasarin suna ciwo bashi ne a banki domin yin noma da kuma kudin ruwan da ake dora masu, asarar za ta yi masu yawa.
Adamu ya ci gaba da cewa, idan manyan manoma ba su yi nom aba a kasar nan, za samu karancin abinci, inda ya ce, hakan ne ya sa zaka ga ana yin kira aje a sawo abinci daga ketare, in an sawo abincin daga ketare, Nijeriya za ta iya yin asara mai yawa domin hakan zai iya dfurkusar da tattalin arzikin kasar nan.
Ya yi nuni da cewa, misali an je an sawo tan miliyan biyu na masara don shigo wa da shi cikin Nijeriya, sai an kashe kusan naira tiriliyan daya, inda ya kara da cewa, a kasar nan, ban da sauran amfanin gona kasar nan na bukatar akalla tan miliyan ashirin.
Ya ce, in har za a sawo masara a kasar waje ba a noma a kasar nan ba, akalla za mu yi asarar zunzurutun kudi kamar naira tirilyan goma, inda yay i nuni da cewa, idan ba a bai wa manoman kasar taimakon da ya dace, ba karamar matsala ce za ta auku ba.
Ya yi kira musamman ga gwamnatin tarayya da gwamnatin jihohi da na kananan hukumomi su mayar da hankali kan bunkasa noman rani, inda ya yi nuni da cewa, ya zama wajibi a samar da kyakyawan tsari, amma idan ba a yi hakan ba, ba mu san irin abin da zai faru a kasar nan ba.
Da yake yin tsokaci kan tsarin da gwamnatin tarayya ta fito da shi, na dakile ‘yan kasuwa na kasar waje zuwa gonakan manoman kasar nan don sayen amfanin gona da suka noma kai tsaye, Makarfi ya ce, wannan tsarina bin yaba wa ne, sai ya sanar da gwamnatin ta makaro domin tun tuni ya kamata a ce an yi irin wannan tsarin.