Shugaban gamayyar kungiyoyin matasan arewa mazauna Legas, Alhaji Ibrahim Ya’u Galadanci ya nuna takaicinsa da damuwarsa kan yadda arewa ke komawa baya a kowanni bangare, musamman a bangaren ci gaban rayuwa.
Ya bayyana cewa bangar siyasa ce sillar rashin ci gaban arewa.
- Za A Sake Yin Gasar Masu Kirkira Da Fasaha Ta Katsina Karo Na Biyu
- Gwamnatin Kaduna Ta Karyata Jita-jitar Malalar ‘Yan Ta’adda Tsakanin Kaduna Da Zariya
Shugaban ya nuna haka ne a tattaunawarsu da wakilinmu, inda ya ce rashin shugabanni nigari a arewa da a kullum babu abun da suke yi illa tura matasa cikin bangar siyasa.
A cewarsa, “Tabbas matasa na da muhimmancin gaske a kowacce al’umma, tasirinsu ya fi gaban a zura ido kawai ga al’amura ko yanayin yadda suke gudanar da rayuwa.
Wajibi ne da ya hau kan al’umma kan yin tattalin rayuwar matasa, samar da hanyoyin shigar da sakonnin abubuwa masu kyau don su siffantu da su, haka kuma a yi musu bayanin illolin abubuwa marasa kyau don su kaurace musu.”
Shugaban a ci gaba da bayyana cewa matsalar bangar siyasa ana samu a ko’ina a Nijeriya da ma duniya baki daya, amma na yankin arewa abun ya wuce misali.
Inda ya kara da cewa, “duk wata kasa da ta ci gaba a wannan duniya, idan aka waiwaiyi sirrin da ke tattare da samuwar ci gabanta, za a ga akwai hannun matasansu yake. Saboda ba su yin sakaci a fannin kulawa da rayuwar matasa ba.
“Hakki ne babba wanda ya rataya a wuyan iyaye namu na arewa da su kasance mataki na farko a inda ‘ya ‘yansu za su koyi tarbiyya, mu’amala da mutane, kiyaye dokokin kasa, kauce wa ayyukan barna da dai sauransu.
“Idan matasamu suka hankalta ta hanyar kauracewa bangar siyasa da rikicin zabe, tabbas baragurbin ‘yan siyasa da ba su son zaman lafiya a Nijeriya ba za su kai ga cimma burinsu ba na zubar da jinin mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba.
“A matsayinka na matashi, ya kamata ‘yan siyasa su taimake ka wurin gina rayuwarka wajen samar da ayyukan da matasa za su yi na bankwana da zaman banza, a samar masu guraben karatu a makarantun da muke da su.
Wannan shi ne aikin gina rayuwar mutum ba a ba shi makami da kwaya ba. Makami da kwaya sai dai rusa rayuwarka, ya zama ba ka da fata nagari ga kanka da al’ummar da kake tare da su” kamar yadda ya fada.
Daga karshe, ya yi kira ga shugabannin siyasar arewa da su sani sai da zaman lafiya za su iya shugabantar al’umma, idan suka dora matasa a bangar siysa ba za a sami zaman lafiya ba.