Gwamnatin jihar Kaduna ta karyata rahoton dake yawo a kafafan sada zumunta dake cewa matafiya su tsaya inda suke kar su bi hanyar Zariya zuwa Kaduna.
Rahoton karyan ya yadu ne yana zargin cewa, wai anga ‘yan bindiga dauke da muggan makamai sun tare hanyar Zariya zuwa Kaduna.
Gwamnatin jihar Kaduna ta karyata wannan rahoton, kuma ta bukaci al’umma da su yi watsi da rade-raden kwata-kwata. Wannan yunkuri ne a fili a nasaka tsoro a zukatan matafiya.
Gwamnatin Jihar Kaduna ta tabbatar wa da ‘yan kasa da matafiya cewa hanyar Kaduna zuwa Zariya Lafiya take.
An yi kira ga al’umma da su ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum, kada su kula da rahoton karya.