Ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta sanar a jiya Juma’a da cewa, fannin “e-commerce”, wato kasuwanci ta yanar gizo na kasar Sin ya samu ci gaba a cikin watanni bakwai na farkon bana, inda aka samu karuwar cinikayyar dimbin kayayyaki ta yanar gizo ko intanet.
A cewar hukumar kididdiga ta kasar, adadin cinikin kayayyaki ta yanar gizo ya karu da kaso 9.2 cikin dari a watanni bakwai na farkon bana, idan an kwatanta da jimillar ta bara.
Ma’aikatar ta ce manyan fannonin da suka haifar da kashe kudi a yanar gizo, sun hada da yadda ake sayen na’urori na fasahar zamani, da tsarin musayar tsoffin kayayyaki da sabbi, inda karuwar da aka samu ta adadin kwamfuta da na’urorin zamani da ake rataya su a jiki da aka sayar da su, ta kai kaso 29.9 da kaso 28.4 cikin dari bisa jimillar ta bara.
A sa’i daya kuma, bangaren amfani da hidimomin da aka samar da su ta yanar gizo ya habaka cikin sauri a cikin wadannan watanni 7, inda yawan kudin da aka kashe a fannonin yawon shakatawa, abinci da nishadin al’adu ya karu da kaso 24.8, da 16.6, da 11 bisa dari, daya bayan daya. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp