Wani rahoton bincike ya nuna cewa, a cikin ‘yan shekarun nan, manyan kamfanonin kera kayayyaki na kasar Sin, sun samu ci gaba matuka, inda kasuwar ta kara samun darajar da fadada tasirinta a kasuwannin ketare.
Rahoton da kungiyar masu kamfanoni ta kasar Sin ta fitar, ya bayyana cewa, ya zuwa ranar 10 ga watan Disamba, yawan kamfanonin kera kayayyaki masu hannun jari dake rukuni na A ko A-share a turance, ya kai 2,121, wanda ya karu da kashi 69.7 bisa dari daga 1,250 a karshen shekarar 2017.
Darajar manyan kamfanonin kera kayayyaki a kasuwa da aka zayyana, sun karu sosai daga shekarar 2017 zuwa ta 2021. Rahoton ya bayyana cewa, wadannan kamfanoni sun samu kudin shiga da yawansu ya kai yuan tiriliyan 11.79 kwatankwacin dalar Amurka tiriliyan 1.69, a cikin kudaden shiga na ayyukan da suka gudana a shekarar 2021, idan aka kwatanta da yuan tiriliyan 7.47 a shekarar 2017.
Rahoton ya nuna cewa, sakamakon yadda suke fadada kasuwanninsu a ketare na tsawon shekaru, kudaden shigar da kamfanonin ke samu daga harkokinsu a kasuwannin ketare, ya kai yuan tiriliyan 27.51 a shekarar 2021, wanda ya karu daga yuan tiriliyan 13.77 da aka yi rajista a shekarar 2017.(Ibrahim)