• English
  • Business News
Sunday, May 25, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Bani Da Wani Buri A Yanzu Da Ya Wuce In Ganni A Dakin Mijina – Khadija Muhammad

by Rabilu Sanusi Bena and Sulaiman
8 months ago
in Nishadi
0
Bani Da Wani Buri A Yanzu Da Ya Wuce In Ganni A Dakin Mijina – Khadija Muhammad
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

A daidai lokacin da wasu suke yayata maganar cewa jarumai mata a masana’antar Kannywood basu fiye son zaman aure ba, Jaruma Khadija Muhammad ta karyata wannan zance kwata-kwata inda ta tabbatar da cewar wannan magana sam babu kamshin gaskiya a cikinta domin kuwa a halin yanzu bata da wani buri da ya wuce ta yi aure ta kuma tare a gidan mijinta.

Jarumar ta yi wannan jawabi ne a wata hira da ta yi da BBC a cikin shirinsu na daga bakin mai ita inda ta bayyana batutuwa da dama da suka dangance ta,kama daga karatunta shigowarta masana’antar Kannywood da sauransu.

  • Lokaci Ya Yi Da Za A Samar Da Sabon Tsarin Mulki – Babban Limamin Coci
  • Gbemisola Yusuf: Daga Sayar Da Ruwa A Filin Wasa Na Agege Zuwa Alkaliyar Wasa

Jaruma Khadija ta ce ita haifaffiyar garin Kano ce a unguwar Kabuga,anan Kabuga ta yi karatun Firamare da Sakandire kafin ta wuce makarantar gaba da Sakandire ta Usman Danfodiyo Unibersity da ke da reshe a Kwalejin Ilimi ta Jihar Kano, ta kuma bayyana cewar ta taba yin aure amma yanzu ba su tare da mijin nata.

Labarai Masu Nasaba

Ban Dauki Harkar Fim Da Wasa Ba -Hauwa Ayawa 

Hukuma Ta Dakatar Da Haska Fina-Finai 22 Har Sai Baba Tagani

Da ake tambayarta a kan ta yaya ta shigo harkar fim, jarumar mai shekaru 30 ta bayyana cewar akwai da dama daga cikin yan unguwarsu ta Kabuga da suke cikin wannan harka ta Kannywood hakan yasa suke yawan shigowa Kabuga domin daukar fina finansu, da haka ne har sha’awar shiga wannan harka ta kama ta har ta nemi shawarar yan uwa da abokan arziki, bayan ta tuntubi gida sai aka amince mata ta fara fim, indata fara fitowa a wani shiri mai suna Dr Bahijja.

Tun daga wannan lokacin Khadija ta fito a manya manyan fina finai a masana’antar ta Kannywood da suka hada da Alaka, Gidan Sarauta da sauransu inda ta bayyana fim din A Duniya da ta fito a matsayin wanda tafi so domin kuwa anan aka fi saninta in ji ta,amma a halin yanzu bata da wani buri da ya wuce tayi aure ta tare a dakin mijinta.

Daga karshe Khadija ta bayyana cewar akwai bukatar jarumai da mahukunta a wannan masana’antar ta Kannywood su samu hadin kai wanda shi kadai ne abinda zai samarwa masana’antar cigaba mai dorewa,inda ta tabbatar da cewa a duk wata tafiya wadda babu hadin kai a tsakanin wadanda suke cikinta babu ta yadda za’a yi wannan tafiya ta ci gaba domin kuwa hadin kai shi ne kashin bayan ci gaban kowace irin tafiya.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: KannywoodTaurarin Mata
ShareTweetSendShare
Previous Post

Hare-haren ‘Yan Bindiga A Sahel Sun Jefa Shugabannin Soji Cikin Zulumi

Next Post

An Saki Daruruwan Fursunoni Daga Gidan Yarin Jamhuriyar Congo Saboda Rashin Lafiya

Related

Ban Dauki Harkar Fim Da Wasa Ba -Hauwa Ayawa 
Nishadi

Ban Dauki Harkar Fim Da Wasa Ba -Hauwa Ayawa 

20 hours ago
Hukuma Ta Dakatar Da Haska Fina-Finai 22 Har Sai Baba Tagani
Nishadi

Hukuma Ta Dakatar Da Haska Fina-Finai 22 Har Sai Baba Tagani

6 days ago
Ban ÆŠauki Harkar Fim Da Wasa Ba – Hauwa Ayawa
Nishadi

Ban ÆŠauki Harkar Fim Da Wasa Ba – Hauwa Ayawa

7 days ago
Har Yanzu Da Bazar Mahaifina Nake Rawa -Hanafi Ibro
Nishadi

Har Yanzu Da Bazar Mahaifina Nake Rawa -Hanafi Ibro

2 weeks ago
Rashin Hadin Kai Ke Dakile Ci Gaban Masana’antar Kannywood -Ayatullahi Tage
Nishadi

Rashin Hadin Kai Ke Dakile Ci Gaban Masana’antar Kannywood -Ayatullahi Tage

2 weeks ago
Ya Kamata Mata ‘Yan Fim Su Rike Mutuncin Kansu – Aisha Tafida Gombe
Nishadi

Ya Kamata Mata ‘Yan Fim Su Rike Mutuncin Kansu – Aisha Tafida Gombe

3 weeks ago
Next Post
An Saki Daruruwan Fursunoni Daga Gidan Yarin Jamhuriyar Congo Saboda Rashin Lafiya

An Saki Daruruwan Fursunoni Daga Gidan Yarin Jamhuriyar Congo Saboda Rashin Lafiya

LABARAI MASU NASABA

Shugaban Hukumar DSS Ya Kaddamar Da Cibiyar Koyar Da Addinin Musulunci A Kaduna 

Shugaban Hukumar DSS Ya Kaddamar Da Cibiyar Koyar Da Addinin Musulunci A Kaduna 

May 25, 2025
Warware Basussuka: WAEC DA NECO Sun Saki Sakamakon ÆŠaliban Zamfara Na Shekara Biyar

Warware Basussuka: WAEC DA NECO Sun Saki Sakamakon ÆŠaliban Zamfara Na Shekara Biyar

May 25, 2025
Shekaru 10, Kofuna 16 Kevin De Bruyne Ya Yi Bankwana Da Manchester City

Shekaru 10, Kofuna 16 Kevin De Bruyne Ya Yi Bankwana Da Manchester City

May 25, 2025
An Gano Kofin Gasar Zakarun Turai Na Mata Bayan Sace Shi Da Aka Yi

An Gano Kofin Gasar Zakarun Turai Na Mata Bayan Sace Shi Da Aka Yi

May 24, 2025
Firaministan Sin Ya Sauka A Indonesia Domin Ziyarar Aiki

Firaministan Sin Ya Sauka A Indonesia Domin Ziyarar Aiki

May 24, 2025
Tawagar MDD Da Majalisar Shugabancin Libya Sun Kafa Kwamitin Tsagaita Bude Wuta

Tawagar MDD Da Majalisar Shugabancin Libya Sun Kafa Kwamitin Tsagaita Bude Wuta

May 24, 2025
Firaministan Sin Ya Shugabanci Taro Kan Masana’antu Masu Amfani Da Makamashi Mai Tsafta Da Kare Muhalli 

Firaministan Sin Ya Shugabanci Taro Kan Masana’antu Masu Amfani Da Makamashi Mai Tsafta Da Kare Muhalli 

May 24, 2025
Yara Miliyan 2.9 A Nijeriya Ke Fama Da Rashin Abinci Mai Gina Jiki – UNICEF

Yara Miliyan 2.9 A Nijeriya Ke Fama Da Rashin Abinci Mai Gina Jiki – UNICEF

May 24, 2025
CHINADA Ta Nuna Matukar Adawa Da Gasar Wasannin Da Aka Amince Da Kwayoyin Kara Kuzari

CHINADA Ta Nuna Matukar Adawa Da Gasar Wasannin Da Aka Amince Da Kwayoyin Kara Kuzari

May 24, 2025

Tsokaci Kan Yadda Wasu Matasa Ke Yin Aure Ba Tare Da Sana’a Ba

May 24, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.