Bankin Duniya ya shirya tsaf domin amincewa da sabon rokon cin bashin dala miliyan 632 da Nijeriya ke nema a daidai kabar da ake ta kukan yawan basukan da ke kan kasar ma sun yi yawa.
Rancen wanda aka shirya ciwo shi domin taimaka wa bangarorin da suka hada da inganta sashin abinci mai gina jiki da samar da ilimi mai inganci a matakin farko.
- Ofishin Siyasa Na Kwamitin Tsakiyar Jks Ya Kira Taron Nazarin Ayyukan Kiyaye Muhallin Halittu Da Sauransu
- Dubban Jama’a Sun Sallaci Gawar Sheikh Idris Dutsen Tanshi
A bayanan da aka samu a shafin bankin dukiyar a ranar Lahadi, ya nuna cewa rancen ya kunshi na dala miliyan 80 da aka ware domin inganta sashin samar da abinci mai gina jikin dan’adam a Nijeriya a shiri na 2.0 da kuma wani rancen dala miliyan 552 da aka nema domin shiri mai hankoron samar da ingancin ilimi a matakin farko ga kowa.
Wannan matakin dai dukkan suna karkashin shirin babban bankin na taimaka wa Nijeriya a bangaren shirinta na samar da ci gaba da suke da manufar kyautata lafiya, ilimi da ci gaban jama’a.
Rancen ana sa ran za su taimaka wa kokarin gwamnatin tarayya na inganta samar da abinci mai gina jiki da kuma inganta samun damar ilimi mai inganci ga yara kanana a Nijeriya.
A halin da ake ciki, tuni ma Bankin Duniya ya riga ya amince da lamunin dala miliyan 500 ga Nijeriya a ranar Juma’ar da ta gabata don tallafa wa shirin kasar na “Community Action for Resilience and Economic Stimulus Programme”.
Samun wannan rancen wani dama ce ga Nijeriya da zai taimaka mata wajen shawo kan matsalolin da suke bangaren tattalin arziki da inganta yanayin rayuwar jama’a, wadata kasa da abinci, da samar da range ga talakawa da kamfanoni.
Kazalika, a wani rancen da Nijeriya ta nema na dala miliyan 800 domin shirin ‘National Social Safety-Net Program Scale Up,’ Bankin Duniyan ya sake wa Nijeriya dala miliyan 315 daga cikin wannan adadin.
Tsawon kusan shekara, Nijeriya ba ta samu wani kudi daga Babban Bankin duniya ba a matsayin rance, tun bayan wanda ta ba ta a watan Disamban 2021. Na samu jinkirin sake kudaden ne sakamakon wasu batutuwa na damfara da aka gano a shirin.
Shugaban kasa Bola Tinubu ya kaddamar da shirin SSN wanda ke da manufar rabar da naira dubu 25,000 ga magidanta miliyan 15 na tsawon watanni uku domin yaki da fatara. Ma’aikatar kula da jin kai da yaki da talauci ne aka daura wa alhakin gudanar da shirin rancen dala miliyan 800 na Bankin Duniyan.
Har ila yau, gwamnatin tarayya ta dakatar da shirin tallafin kudi na (cash transfer programme) domin gudanar da bincike kan zarge-zargen almundahana da ke makale da shirin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp