Bankin TAJ mai gudanar da harkokinsa da ke bunkasa cikin sauri ta hanyar fasaha, ya kafa sabon tarihi sama da shekara 100 ba a samu irinsa ba.
A cikin shekaru uku da kafa Bankin TAJ, ya samu nasarar biyan riba ga masu hannun jari.
- A Karon Farko Sanata Barau Ya Jagoranci Zaman Majalisar Dattawan Nijeriya
- Jihohi 14 Da Za Su Fuskanci Ambaliyar Ruwa —NEMA
Idan za a iya tunawa, Bankin TAJ ya kafa tarihi a farkon wannan shekarar a matsayin bankin na farko a tarihin Nijeriya da ya jera tsarin manuni na Sukuk a kan kasuwar hada-hadar kudi ta Nijeriya bayan samun nasarar fitar da shi.
Bayanan da aka samu daga rahoton kudade na bankin kasuwanci ya nuna cewa babu wani banki da ya samu irin wannan gagarumin nasara irin wannan a cikin sama da shekaru 100 na tarihin harkokin kudade.
Da yake jawabi ga masu hannun jarin a wajen taron, shugaban gudanarwar bankin, Alhaji Tanko Isiaku Gwamna, ya ba da labarin guguwar tattalin arzikin duniya a cikin shekaru biyu da suka gabata, da kuma ci gaban tattalin arzikin kasa da aka samu a fanni, musamman hauhawar farashin kayayyaki wanda ya yi illa ga harkokin kasuwanci.
Gwamna ya ci gaba da cewa, duk da yanayin da ake ciki na rashin aikin yi, hukumar gudanarwar bankin za su yi kokarin kirkiro da dabaru masu muhimmanci da za su ci gaba da dora Bankin TAJ a kan turbar da ta tace domin amfanin masu hannun jari da kuma tattalin arzikin Nijeriya.
Dangane da batun rabon ribar, ya ce, “A madadin hukumar gudanarwa, ina farin cikin sanar da masu hannun jarinmu cewa mun ba da shawarar a biya rarar kashi 1 ga kowane hannun jari 10, bisa amincewar masu hannun jari. Za mu ci gaba da jajircewa wajen inganta fadada kasuwanci da samun nasara tare da tabbatar da cewa an kebe maku adadi mai yawa na ribar da muka samu.”
A cikin rahotonsa, shugaban bankin, Mista Hamid Joda, ya bayyana cewa harkokin kudade a 2022 yana da matukar muhimmi ga ci gaba a cikin tafiyar masu ba da bashi babu ruwa duk da irin kalubalen da aka samu na nuna yanayin aiki, amma an samu nasarar cimma abubuwa masu yawa.
Dangane da harkokin kudade na bankin a cikin 2022, Joda ya ruwaito cewa Bankin TAJ ya samu karuwa a cikin muhimman abubuwa a shekarar, yayin da ma’auni ya karu da sama da 93 daga Naira biliyan 110 da aka samu na 2021 zuwa Naira biliyan 212, yayin da riba kafin fitar da haraji ya karu daga Naira biliyan 1.6 a 2021 zuwa Naira biliyan 5.081 biliyan a shekarar kudi ta 2022.
Ya kuma shaida wa masu hannun jarin cewa ribar da bankin ke samu a kowanne kaso ya karu da kashi 138 zuwa Naira 31.27 a 2022, idan aka kwatanta da Naira 13.11 da aka samu a shekarar 2021.
Game da shirye-shiryen kara bunkasa harkokin bankin nan da shekaru masu zuwa kuwa, Joda ya ce, “A kokarin da muke yi na inganta kayayyakin da ake samu ribar da babu ruwa da kuma tsarin hada-hadar banki a duk fadin kasar nan, hukumar gudanarwar ta Bankin TAJ sun kafa muhimman manufofi da za a bi a shekarar 2023.
“Muna shirin bude rassa da ofisoshin kasuwanci 110 a fadin manyan biranen jihohi da manyan cibiyoyin kasuwanci kafin shekarar 2024 da kuma bayar da kayayyaki da ayyuka na banki da babu ruwa ga kasuwanni, domin habaka hanyar sadarwar hukumarmu zuwa wakilai masu aiki 100,000 nan da 2025, don rage matsalolin harkokin kudi tare da habaka abokanan kasuwanci zuwa akalla miliyan hudu nan da 2027, saboda cimma bukatar mafi karancin gamsuwar abokin ciniki na kashi 85,” in ji shi.
Da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan taron, kwararre kan harkokin kudi, Alhaji Tata Shekaru Omar, ya yaba wa hukumar gudanarwa bisa sabbin tsare-tsare da suka sanya har Bankin TAJ ya zama na sahun gaba a harkokin hada-hadar kudi na kasar nan.
Ya ce, “Bankin TAJ bai cika shekara hudu da kafawa ba, amma ya samu gagarumar riba a shekararsa ta farko da ya fara aiki, labari ne mai dadi da farin ciki ga duk masu hannun jari a bankin. Ina so in yi godiya ga shugaban bankin da daukacin tawagarsa da suka yi irin wannan aiki, musamman yadda bankin ke ba da riba ga masu hannun jari.”