Ko shakka babu, 2023 shekara ce da ta kasance mai matukar tarihi da ‘yan Nijeriya ba za su taba iya mantawa da ita ba a siyasance. shekara ce da ‘yan Nijeriya suka fito kwansu da kwarkwatansu suka zabi sabon shugaban kasa da zai jagoranci gwamnatin tarayya na tsawon shekara hudu tare da wasu gwamnonin jihohi a cikin kasar nan.
Lallai wannan shekara ce da ‘yan Nijeriya ba za su iya mantawa da ita ba cikin gaggawa, domin al’amuran siyasa ne suka karade shekarar wanda ba a saba gani a wasu shekaru ba. Ga wasu daga cikin manyan batutuwan siyasa da suka karade shekarar 2023 kamar haka:
- An Kashe Mutane 700, An Lalata Kauyuka 50 Cikin Wata 3 A Mazabata — Sanata
- Wadanda Suka Jikkata Yayin Girgizar Kasa A Kasar Sin Sun Samu Kulawar Da Ta Dace
- Zaben Shugaban Kasa
An gudanar da zaben shugaban kasa a ranar 25 ga watan Fabrairu a fadin kananan hukumomin kasar nan guda 774, tare da wasu kalubale. A karon farko, an gwada sabuwar doka da aka fi sani da dokar Zabe ta 2022. Kafin kada kuri’a, ‘yan Nijeriya na da kwarin giwar kan hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) dangane da yadda ta gudanar da shirye-shirye da kuma bai wa mutane tabbacin yin amfani da na’ura wajen bayyana sakamakon zabe tun daga rumfunan zabe har zuwa cibiyoyin amsan sakamakon, kamar dai yadda dokar zabe ta tanada.
‘Yan Nijeriya da dama suna ganin watsa sakamakon zabe kai tsaye ta na’urar wani yunkuri ne da zai rage magudin zabe a Nijeriya. Duk da cewa an yi aiki da wannan lamari a zaben ‘yan majalisar dokokin kasa da zaben gwamna da na ‘yan majalisun jihohi, amma lamarin ya samu nakasu a zaben shugaban kasa da aka fara gabatarwa.
Daga karshe dai, INEC ta ayyana Bola Tinubu na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa, wanda ya kasance shugaban Nijeriya na 16. A cewar INEC, Tinubu ya samu kuri’u 8,794,726, wanda ke nuna kashi 37 cikin 100 na yawan kuri’un da aka kada, inda ya doke Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP, wanda ya samu kuri’u 6,984,520, wanda ya samu 29 cikin 100 na kuri’un da aka kada, sannan ya kasance a na biyu , da Peter Obi na jam’iyyar LP wanda ya samu kuri’u 6,101,533 ko kuma kashi 25 na kuri’un da aka kada, wanda ya zaman a uku a zaben.
Sai dai kuma Atiku da Obi sun yi watsi da ayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa, inda suka garzaya kutuna, tun daga kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa da kotun daukaka kara har zuwa kotun koli, wadda ta tabbatar da zaben a matsayin wanda ya dace da ka’idojin da ake bukata tare da watsi da korafe-korafensu da suka shigar a gaban kotun.
A ranar 29 ga watan Mayun 2023, aka rantsar da Tinubu a matsayin zababben shugaban kasa, wanda cikin jawabinsa na farko ya cire tallafin man fetur. Masana na ganin cire tallafin man ya kara jefa ‘yan Nijeriya cikin mawuyacin hali, tun daga tsadar rayuwa da hauhawar farashin kayayyaki da na sufuri da dai sauransu.
Haka zalika, a ranar 18 ga Maris, 2023, an gudanar da zaben gwamnoni da na ‘yan majalisar dokoki a wasu jihohi da ke fadin kasar nan, wanda a nan ma an samu korafe-korafe wanda ta kai ga shigar da kararraki tun daga kotunan sauraron kararrakin zabe har sai da ta dangana ga kotun koli.
Har ila yau, INEC ta gudanar da zaben gwamna a ranar 11 ga watan Nuwamba a jihohin Bayelsa, Kogi, da Imo, yayin da, APC ta ci gaba da rike jihohin Imo da Kogi, wanda aka zabi Gwamna Hope Uzodimma karo na biyu da Ahmed Ododo. Sai dai PDP a Bayelsa ta ci gaba da rike kambunta, wanda gwamna Duoye Diri ya yi nasara aka zabe shi karo na biyu, inda ya doke abokin karawarsa na jam’iyyar APC, Timipre Sylba.
- Hukuncin Kotun Daukaka Kara A Shari’ar Zaben Gwamna A Wasu Jihohi
Kotun daukaka kara ta soke nasarar Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal da Gwamnan Filato, Caleb Mutfwang da Gwamnan Kano, Abba Yusuf, wadda ta bayyana cewa zaben nasu bai yi daidai da tsarin dokar zabe ba.
A yayin da kotun daukaka kara da ke Abuja ta kori gwamna Lawal tare da bayyana zaben gwamnan Jihar Zamfara da aka yi a watan Maris a matsayin wanda bai kammala ba, ta yi nuni da cewa gwamnan Jihar Filato ba cikakken dan jam’iyyar PDP ba ne.
Haka kuma, kotun daukaka kara ta soke zaben gwamnan Jihar Kano bayan ta gano cewa ba asalin dan jam’iyyar NNPP ba ne. Kotun ta amince da hukuncin da karamar kotun sauraron kararrakin zabe ta yanke wanda tun farko ta soke zaben gwamnan tare da bai wa dan takarar jam’iyyar APC, Nasiru Yusuf Gawuna nasara a zabe.
- Dambarwar Ayyana Binani A Matsayin Gwamnar Adamawa
Zaben gwamnan Jihar Adamawa na ranar 18 ga watan Maris, na daya daga cikin abubuwan da suka fi daukar hankali a shekarar 2023. Gwamna mai ci kuma dan takarar jam’iyyar PDP, Ahmadu Fintiri, ya samu kuri’u 31,249 sama da babban abokin hamayyarsa Aisha Binani Dahiru na jam’iyyar APC. Bayan kammala tattara sakamakon zaben kananan hukumomi 10, Fintiri yana kan gaba, yayin da ake ci gaba da tattara sakamakon zaben, kwamishinan zabe na Jihar Adamawa, Hudu Yunusa-Ari, ya isa cibiyar tattara sakamakon zaben, inda ya bayyana Binani a matsayin wanda ta lashe zaben gwamnan jihar.
Baya ya ayyana Binani a matsayin gwamnan Adamawa, an sanar da cewa ba aikin Yunusa-Ari ba ne ya bayyana wanda ya lashe zaben, Mele Lamido wanda shi ne jami’in tattara sakamakon zabe ke da hakkin sanar da sakamakon zaben. Bayan samun wannan bambarwar, tsohon kwamishinan Adamawan ya shiga wasan boya da mahukunta, amma daga baya an samu nasarar damke shi kuma a halin yanzu yana fuskantar tuhuma.
- Zaben Shugabancin Majalisar Dattawa
Shugabancin majalisar dattijai ta 10, wani lamari ne da aka yi ta ce-ce-ku-ce, wanda ya hada wasu tsoffin gwamnoni uku da suka hada da Godswill Akpabio, Orji Kalu da Abdulaziz Yari, inda suka shiga takara a tsakaninsu domin samun damar zama shugaban majalisar dattawa ta 10.
Daga baya Kalu ya janye takararsa bayan da ya gabatar da jawabi mai muhimmanci a taron rufe majalisar dattawa ta 9.
Sa’o’i kadan gabanin zaben shugaban majalisa ta 10, Kalu ya janye muradinsa tare da mara wa Yari baya, wanda daga bisani Akpabio ya samu nasarar zama shugaban majalisar dattawa na 10.
- Zaben Shugaban Majalisar Wakilai
Kamar dai yadda ya faru a zauren majalisar dattawa, shugabancin majalisar wakilai ya ci karo da hamayya a tsakanin ‘yan siyasa. A cikin wadanda suka nuna sha’awarsu na samun shugabancin majalisar wakilan dai sun hada da Yusuf Gagdi, Muktar Betara da Tajudeen Abbas. Sai dai daga bisani Abbas ne ya samu nasara, wanda wasu ke ganin shi ne zabin da fadar gwamnati ta yi.
Saura lokaci kadan kafin fara zaben Gagdi da Betara sun janye, amma Abbas ya kara da irin su Sani Jaji da Ahmed Wase. A lokacin zaben Jaji da Wase sun samu kuri’u uku kowanne, wanda hakan ya nuna gagarumin rinjaye da Abbas mai wakiltar mazabar Zariya ta Jihar Kaduna a karkashin jam’iyyar APC ya lashe zaben.
- Dambarwar Rashin Bai Wa el-Rufai Mukamin Minista
Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir el-Rufai na daya daga cikin fitattun jiga-jigan jam’iyyar APC da suka taka muhimmiyar rawa wajen ganin gwamnatin Tinubu ta samu nasara. Bayan da Tinubu ya hau kan karagar mulki, el-Rufai yana daga cikin wadanda aka zaba domin ba su mukamin minista. A lokacin da ya gurfana a zauren majalisar dattawa domin tantance shi, ya dai amsa tambayoyin da suka shafi batutuwa da kalubale a fannin wutar lantarkin Nijeriya. Sai dai ba zato ba tsammani, sakamakon rahoton tsaro ya hana el-Rufai samun mukamin minista.
Da alama dai sun nuna cewa na kusa da shugaban kasa Tinubu ne suka yi masa makirci na rashin samun mukamin minister. Sai dai kuma tsohon ministan Babban Birnin tarayya Abuja ya rungumi kiddara, inda daga baya ya fice daga kasar.
Wasu masu sharhi kan harkokin siyasa na ganin cewa hana el-Rufai minista da kuma wasu ‘yan siyasa da suka tura mota ta bade su da hayaki hakan bai dace ba.
- Rikicin Siyasa Tsakanin Obaseki Da Shaibu
A shekarar ce, rikicin siyasa ta yi kamari tsakanin mataimakin gwamnan Jihar Edo, Philip Shaibu da ubangidansa, gwamnan Jihar Edo, Godwin Obaseki. Ya dai bi ubangidansa zuwa jam’iyyar PDP tare da barin tafiyar Osagie Ize-Iyamu na jam’iyyar APC mai samun goyon bayan Adams Oshiomhole domin ci gaba da rike kujerar gwamnan jihar.
Saboda haka, ‘yan siyasa guda biyu sun raba gari ne lokacin da Shaibu ya nuna muradinsa na ya gaji maigidansa a zaben gwamnan Edo a 2024, wannan shi ne babban dalilin rashin jituwar da ke tsakaninsu a halin yanzu. Obaseki dai yana son mulki ya koma yankin Edo ta tsakiya, inda kuma Shaibu ya fito ne daga yankin Edo ta Arewa, inda ya ce idan har hakan ta faru, lallai jam’iyyarsa ta PDP ba ta yi wa yankinsa adalci ba.
Makonnin da suka gabata ya garzaya wata babbar kotun Abuja, inda ya nemi a hana Obaseki tsige shi daga kan kujerar mataimakin gwamna. Duk da cewa daga baya ya janye karar, an dai saka kafar wando daya da mataimakin wanda suka hada da rashin biyan alawus-alawus na ofishinsa da kuma fitar da ofishin mataimakin gwamna daga gidan gwamnati da dai sauransu.
- Rikicin Siyasar Jihar Ribas
Kamar dai Jihar Edo, Jihar Ribas ita ma ta shiga cikin rikicin siyasa a shekarar 2023. Kasa da wata bakwai bayan kammala zabe, Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike ya fahimci cewa biyayyar da yake tsammanin samu daga wurin magajinsa, Gwamna Siminalayi Fubara tana kara dusashewa a hankali.
Rahotanni da dama na nuni da cewa tun bayan rantsar da shi a matsayin gwamna, Fubara yana son a bar shi shi kadai ya aiwatar da ajandarsa na kawo sauyi ga rayuwar mutanen Jihar Ribas. Amma Wike ya yi ikirarin tsoma baki a harkokin gwamnatin Fubara. A daidai lokacin da rikicin siyasar ta yi kamari tsakanin gwamnan da ubangidansa, kimanin kwamishinoni bakwai da masu rike da manyan mukamai na gwamnatin Jihar Ribas ne suka yi murabus daga majalisar zartarwar gwamnan. Hakan dai ya biyo bayan sauya shekar da ‘yan majalisa 27 suka yi daga PDP zuwa APC, lamarin da ya sa gwamnan ya gabatar da kudirin kasafin kudin 2024 na naira biliyan 800 ga ‘yan majalisar jihar guda hudu.
Wannan rikicin siyasar na Jihar Ribas ta kai ga sai da Shugaban kasa Tinubu ya shiga tsakani, inda ake ganin cewa har yanzu akwai sauran rina a kaba.
- Rikicin Siyasar Jihar Ondo
A Jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa ya zama mukaddashin gwamnan jihar ne bayan da Shugaba Tinubu ya shiga tsakani a kan rikicin siyasar da ya shafe watanni da dama sakamakon Gwamna Rotimi Akeredolu na fama da rashin lafiya.
Akeredolu ya rubuta wa majalisar dokokin jihar cewa zai koma kasar Jamus domin duba lafiyarsa. Gwamnan da ke fama da rashin lafiya ya fara zuwa Jamus neman magani a watan Yuni kuma ya dawo a watan Satumba. A tsawon watanni uku da ya yi baya, mataimakinsa ya yi aiki a matsayin mukaddashin gwamna.
Amma rahotanni sun nuna cewa rashin jituwar da ke tsakaninsa da mataimakinsa ya bayyana bayan da ya kori dukkan jami’an mataimakinsa kan harkokin yada labarai, inda majalisar ta matsa kaimi kan tsige Aiyedatiwa bisa zarginsa da aikata wani babban laifi yayin da yake rike da mukamin gwamna.
To sai dai kuma duk da rikicin siyasar da ke tsakani, Aiyedatiwa, a karo na biyu ya sake hawa kujerar mukaddashin gwamnan jihar.
Babu shakka wadannan su ne wasu daga cikin manyan al’amuran siyasa da suka faru a 2023, kuma wasu za su zarce zuwa 2024. Wasu daga cikin wadannan manyan batutuwan za su tabbatar da inda kasar ta dosa a siyasance a rubu’in farko na shekarar 2024.