Shugabar Gidauniyar Zhulaifat da ke tallafa wa mata da kananan yara da kuma marasa galihu da ke da shalkwata a Jihar Kaduna, Hajiya Aisha Abubakar ta bayyana cewa wasu baragurbin jami’an da ke aiki a hukumomin gwamnati a sassan da ke kare hakkin yara kanana ne ke janyo koma baya ga ayyukan da kungiyoyin da ke bin diddigin cin zarafin yara kanana.
Shugabar Gidauniyar Zhulaifat ta sanar da hakan a hirarta da LEADERSHIP HAUSA a Kaduna.
Aisha ta ce, “Amma mu a gidauniyarmu idan mutane sun kawo mana korafin na cin zarafin yara kanana ko kuma ‘ya’ya mata da wasu batagaren mutane suka yi, ba na yin kasa a gwiwa domin wajen bi masu hakkinsu a gaban hukumomin da abin ya rataya a wuyansu.
“Sai dai a yanzu ana samun raguwar yadda ake cin zarafin yara kanana sabanin a baya, amma an samu a watan da ta gabata, inda wani dan shekara 55 da aka kama shi bisa zargin yunkurin yi wa wasu ‘ya’ya mata fade ta hanyar jan ra’ayinsu da biskit, a yanzu haka muna ci gaba da bin diddin lamarin”.
A cewar Hajiya Aisha, wasu gurbatattun jami’an da ke aiki a wasu ma’aitaun na gwamnti da aka dora wa nauyin hakkin sa ido kan kare cin zarafin yara, akwai wadanda suka yi kaurin suna wajen yin zagon kasa kan bin diddigin cin zarafin yaran.
Hajiya Aisha ta yi kira ga iyaye maza da mata da su tabbatar da suma sa ido a kan ‘ya’yansu. Ta ce bai kuma kamata iyaye maza su bar tarbiyar ‘ya’yansu kawai a hannun matansu ba, domin suma iyayen maza hakki ne su sa ido a kan tarbiyar yaran.
A karshe, Hajiya Aisha ta sanar da cewa ya kamata iyaye su dinga kai ziyara a marantun da ‘ya’yansu ke zuwa neman ilimi, musamman a makarantu boko don su tabbatar da cewa ‘ya’yansu na zuwa makaranta ba yawon banza ba.