A yayin da Nijeriya ta bi sahun sauran kasashen duniya domin yin bikin zagayowar ranar kawo karshen cin zarfin da ake yi wa ‘yan jarida, ana ci gaba da ankarar da al’umma kan gudunmawar da ‘yan jarida ke bayar wa wajen wanzar da tsarin mulkin dimokiradiyya.
Tabbas, cin gashin kowane irin mulikin dimokiradiyya, ya danganta ne, da goyon bayan da kwararrun ‘yan jarida ke bayar wa, musamman ma ta hanyar damar da kafafen yada labarai ke bai wa al’umma su fadi ra’ayoyinsu, ta hanyar fadakarwa, ilimantawa, wanda hakan zai bayar da damar, yin muhawara a kan wani batu, da ya shafi kasa baki daya.
- Cire Tallafin Man Fetur Ya Kawo Ƙarshen Fasa-ƙwauri, in ji NSA
- Gwamnatin Tarayya Za Ta Karbo Bashin Dala 2.2bn Don Bunkasa Tattalin Arziki
A cewar hukumar kula da ilimi da al’adu da kimiyya ta majalisar dinkin duniya wato UNESCO, ta yi nuni da cewa, kawo karshen cin zarafin ‘yan jarida, wani abu ne, da babban kalubale da ake fuskanta a ‘yan kwanukan baya.
Wannan jaridar, tana sane da yadda ‘yan jarida da kafafen yada labarai ke shiga cikin hadari, a yayin da suke kan gudanar da ayyukansu, musamman ma yadda ake azabtar da su, garkame su a gidan Yari ba bisa ka’ida ba, sace su, ciki har da hallaka su, saboda kawai sun wallafa labarai wadanda suka tabbatar da cewa, sahihai ne.
Irin wannan hatsarin da ‘yan jaridar kasar ke tsintar kansu a ciki ne, ya sanya wasu masu ruwa da tsaki, ciki har da kungiyoyin da ke ta fafutukar kare ‘yancin ‘yan Adam, suka bukaci gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu, da ta lalubo da mafita a kan hare-haren da ake kai wa a kan ‘yan jarida da suke gudanar da ayyukansu a fadin kasar.
A kiran da suka yi karo na biyu wanda yake kunshe a cikin sanarwar da suka fitar, Cibiyar bunkasa aikin jarida CJID, CG, gamayyar kungiyoyin ‘yan jarida 85 da kuma wasu masu kishin kasa da wasu kwararrun ‘yan jarida, sun bukaci da a gaggauta kawo karshen yawan kai wa ‘yan jarida hare-hare da cin zarafinsu a daukacin fadin Nijeriya.
Sai dai, daga shekarar 2017 zuwa gaba, hukumar UNESCO ta ce, an samu raguwar kisan da ake yiwa ‘yan jarida a yankunan da tashe-tsahen hankula suka auku.
UNESCO a wata bibiyar bayanai da ta gudanar a 2023, ta ce, sama da ‘yan jarida 50 ne aka hallaka, a yankunna da aka samu tashe-tashen hankula, wanda hakan ya karu a zangon farko na shekarar 2024.
Daga shekarun 2006 zuwa 2024, sama da ‘yan jarida 1,700 ne aka kashe a fadin duniya, wadanda kuma kusan kashi tara ne, daga cikin goma, da suka yi saura, a bangaren Shari’a an gaza warware maganar.
Bisa kididdigar Cibiyar CJID kan harin da aka kai wa ‘yan jarida a Nijeriya, sun kai 51.
CJID ta ce, bisa nazarin da ta yi ta ce, kashi 37 na aukuwar wadannan lamurran sun faru ne daga ranar 1 zuwa ranar 30 na watan Yunin shekarar 2024, wanda hakan ya nuna karuwar lamarin ne.
Kazalika ma, tun bayan wasikar farko ta kai harin a kan ‘yan jarida da CJID ta aika, Cibiyar ta tattara adadin hare-hare a kan ‘yan jarida da ta tabbar sun kai 90 daga ranar 1 na watan Yuli zuwa ranar 22 ga watan Oktobar 2024.
A bangaren alkalumman Cibiyar kare ‘yan jarida ta kasa da kasa kuwa wato Press IPC ta ce, sama da ‘yan jarida 40 aka kai wa hare-hare a Nijeriya a cikin watan tara na shekarar 2024.
Hukumar ta UNESCO ta lura da cewa, hare-haren da aka kai wa ‘yan jarida a Nijeriya na ci gaba da jefa fargaba ga kafafen yada labarai, musamman ma wajen gudanar da ayyukansu.
Kazalika ma, ci gaba da take ‘yancin ‘yan jarida a Nijeiya da wasu masu ruwa da tsaki ke yi, hakan na kara haifar da tararrabi kan kariyar da ta kamata su samu wanda hakan kuma ke zamowa wata barazanar da mulkin dimokiradiyya da samun damar fadar ra’ayi.
Bugu da kari kuma, wannan jaridar ta goyi bayan yunkurin da wadannan kungiyoyin kan kiraye-kirayen da suka yiwa gwamnatin tarayya na ta wanzar da dokoki da kuma daukar matakan bai wa ‘yan jarida kariya da kuma gudanar da aikinsu, ba tare da jin wani tsoro ba, ko fargaba ko kai masu hare-hare ba.
Wannan ya hada da gudanar da zurzurfan gudanar da bincike kan garkame ‘yan jarida da hare-haren da aka kai masu, sannan kuma a tabbatar da duk wadanda suka aikata masu wannan ta’asar, an tuhume su da hukuntawa.
Bugu da kari ma, akwai kuma bukatar a tilastawa bangaren gwamnati domin ta rinka mutunta ‘yancin ‘yan jarida da ba su kariya kamar yadda kundin tsarin mulkin Nijeriya, ya tanadar.
Hakanan ma da, akwai bukatar kafafaen yada labarai su tattauna da jami’an tsaro, musamman ma sojoji, ‘yan sanda, DSS, kan gudunmawar da za su bada ta kare rayukan ‘yan jarida.
Akwai bukatar shugaban kasa Tinubu, ya bayar da umarni kan korafe-korafen a kan jarida domin hukumar da ke karbar korafe-korafen cin zarafin ‘yan jarida da (NMCC), ta gudanar da bincike.
Yin hakan ya zama wajibi ne, musamman domin a tabbatar da ana gudanar da shugabanci nagari da kuma isar da bayanai ga ‘yan kasar.
A ranar 2 ga watan Nuwamba ne, Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya ya ware, a matsayin ranar cin zarafin ‘yan jarida ta duniya wadda ta ke da matsya mai lambar A/RES/68/163.
An dai zabo ranar ta biyo bayan kisan gillar da aka yiwa ‘yan jarida biyu ‘yan kasar Faransa a kasar Mali ranar 2 ga watan Nuwamba 2013.
Bikin ranar ta duniya ya bana, ya guda ne, daga ranar 6 zuwa 7 na Nuwambar 2024 a shalkwatar tarayyar Afirka AU da ke a babban birnin Addis Ababa, na kasar Ethiopia.
Taken bikin na bana shi ne, ‘bai wa ‘’yan jarida kariyar gaggawa a yayin dauko rahotanni a yankunan da ake yin rikice-rikice’’.