Tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani, ya mayar da martani kan barazanar kai hari Abuja.
Sani ya ce ‘yan ta’adda ba sa bayyana rana, wuri da lokacin da za su kai farmaki.
- Xi Ya Jagoranci Shugabannin JKS Zuwa Tsohuwar Hedkwatar Jam’iyyar
- NEDC Ta Raba Wa Mutanen Da Ambaliyar Ruwa Ta Shafa Kayan Abinci A Jihar Bauchi
Kalaman nasa na zuwa ne a daidai lokacin da rahotannin tsaro na Amurka, Birtaniya, Kanada da Ostireliya suka bayar na cewa ana fuskantar barazanar hare-haren ta’addanci a babban birnin Nijeriya.
Gargadin ya ce za a kai hare-haren ne kan gine-ginen gwamnati, wuraren ibada, makarantu da sauran cibiyoyi da jama’a da dama ke taruwa.
Da yake mayar da martani, tsohon dan majalisar ya lura da yadda jami’an tsaro suka kara yawa a Abuja.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Sani ya bukaci ‘yan Nijeriya da su yi taka tsantsan.
Ya wallafa a shafinsa na twitter cewa: “Ko da yake gwamnatin tarayya ta yi watsi da sanarwar tsaron Amurka, na lura da wasu karin jami’an tsaro a babban birnin.
‘Yan ta’adda ba sa sanar da rana, wuri da lokacin da za su kai hari. Dole ne mu ci gaba da taka tsantsan.”