Gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas, ya bukaci a tura masa Bataliyar soji a jihar domin kwato wuraren da ‘yan ta’adda ke yadda suke so a wasu yankunan jihar.
Ya yi wannan rokon ne a ziyarar da ya kai wa babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, a hedikwatar sojoji da ke Abuja.
- Minista: Magajin El-Rufai Ya Yanke Jiki Ya Fadi A Majalisa
- Mafarauta Sun Ceto Mutane 2 Da Aka Sace A Abuja
Gwamnan ya yi alkawarin samar da duk abinda ake bukata don karbar bataliyar a jiharsa.
LEADERSHIP ta rahoto cewa, Bataliya – tana dauke da dakarun soji 300 zuwa 1,000.
A nasa jawabin, babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja ya yi alkawarin tura karin dakarun soji zuwa jihar Taraba.
Sai dai ya yi nuni da cewa, akwai wata bataliya a yankin Arewa maso Gabashin kasar nan a jihar Borno, amma dai ya yi alkawarin samar da karin wata tawagar gaggawa ta sojin zuwa jihar Taraba.