Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ce kan gaba a matakin wadda aka ci karancin kwallaye a tsakanin manyan gasar Turai biyar a kakar nan da ake ciki inda kawo yanzu kwallo bakwai ce ta shiga ragar Barcelona a La Liga, bayan wasanni 20 da aka yi a bana a Sifaniya.
Wannan kwazon ya sa Barcelona, wadda ke jan ragamar teburin La Liga ta bai wa Real Madrid tazarar maki 11, wadda ke biye da ita haka kuma Barcelona ta yi wasa 15 a dukkan fafatawa a bana ba a doke ta ba, wadda ta dauki Spanish Super Cup a Saudi Arabia cikin watan Janairu.
- Da Dumi-Dumi: CBN Ya Umarci Bankuna Su Ci Gaba Da Karbar Tsoffin Kudi
- Karancin Kudi: Ka Tausaya Wa Talakawa Halin Da Suke Ciki, Soludo Ga Buhari
Kungiyar ta kai zagayen dab da karshe a Copa del Rey, za kuma ta yi gumurzu da Real Madrid a wasan hamayya na El Clasico sai dai ana dora alhakin wannan kokarin da kokarin mai koyarwa Dabi.
Kungiya ta biyu a Turai da ba a ci ta kwallaye da yawa a Turai ba, ita ce Newcastle United, wadda 12 suka shiga ragarta kawo yanzu amma an ci Real Madrid kwallo 17 a La Ligar kakar nan, Atletico Madrid ma 17 aka zura mata a raga da Real Sociedad da kwallo 19 ta shiga ragarta.
Bayan wasa 20 a La Liga, Barcelona ta ci kwallo 42, Real Madrid kuwa 40 ta zura a raga kawo yanzu.