ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, July 16, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tsokaci A Kan Illolin Shagwabar Da Kakanni Ke Wa Jikokinsu

by Rabi'at Sidi Bala
3 years ago
Jikoki

Kamar kullum dai shafin TASKIRA na tafe da Tsokaci na musamman, inda ya ke zakulo muku batutuwa daban-daban da suka shafi al’umma dan tattaunawa a kai.

Tsokacinmu na yau zai yi duba ne game da irin matsalolin da wasu ma’auratan ke fuskanta a kan `ya’yansu, musamman ta bangaren Sirikansu (kakannin yaran), ta yadda kakannin ke shawaba yaro, ta hana uwar yaro dukan danta ko da kuwa ya yi kuskuren da za a dake shi.

  • “Akwai Masu Shekara 18 Zuwa 20 Ba Tare Da Hukunci Ba A Gidan Gyaran Hali Na Kuje”
  • PDP Ta Nemi Buhari Da Ya Tilasta Wa ‘Yan APC Su Saki Sabbin Kudin Da Suka Boye Don Sayen Kuri’u

Da yawan wasu kakannin na hana kowa dukan jikansu komai tsananin laifin da yaro zai aikata, wanda dalilin dukan yaron wasu iyayen ke fuskantar mutuwar aure wajen mazajensu ko kuma karin aure, sakamakon kakar yaron ta ba wa danta umarnin hakan.

ADVERTISEMENT

Dalilin hakan ya sa wannan shafi ya ji ta bakin wasu daga cikin mabiyansa game da wannan matsala; Ko mece ce ribar yin hakan ko akasin hakan? Wacce irin matsala hakan za ta iya haifarwa? Ga dai ra’ayoyin nasu kamar haka:

Sunana Mansur Usman Sufi (Sarkin Marubutan Yaki) daga Jihar Kano Nijeriya:

LABARAI MASU NASABA

Ra’ayin Al’umma Game Da Shirin Gwamnati Na Sake Fasalin Hukumar NYSC

Ko Kafa Ƴansandan Jihohi Zai Taimaka Wajen Kawo Ƙarshen Matsalolin Tsaro?

Jikoki
Mansur Usman Sufi

Gaskiya wannan matsalar tana ci min tuwo a kwarya, domin rashin daukar mataki na hukunci akan yara. Kuma idan an dake su kakanni ko iyayensu maza na jin zafi karshe har su raba aure tsakaninsu da mahaifansu. Hakika hakan yana matukar lalata makomar tarbiyyar al’ummar mu, domin kuwa mafiya yawan yaran da suka lalace wannan ne sila, Allah ya gyara mana Amin. Babu wata riba a cikin aikata hakan gaskiya, domin sai ka yarda ka hukunta naka sannan zai gyaru a cikin al’umma. Daga cikin matsalolin da hakan zai haifar su ne; Raini tsakanin yara da mahaifinsu, Rashin tarbiyya, Rashin girmama manya, Wulakanta sauran al’umma. Shawara ita ce; su daina aikata hakan, domin ba abu ne mai kyau ba. Fatan Allah ya gyara mana, ya kuma inganta rayuwar mu.

Sunana Zahra’u Sa’eed daga Jihar Kano:

Jikoki
Zahra’u Sa’eed

Wasu iyayen suna yin hakan ne saboda kauna, kuma gaskiya wannan ba kauna bace, ya kan janyo lalacewar yara da dama za ka ga yaran ba me fada musu su ji. Akasin hakan na jawo lalacewar yaran da kuma rashin wadatacciyar tarbiyya ga yaran. Gaskiya zai iya haifar da matsaloli kamar ga ‘ya’ya mata rashin kamun kai, da kuma rashin zuwa makaranta, da kuma raina iyayen nasu mata, ga maza kuma shaye-shaye da sauransu. Gaskiya shawarata shi ne; iyaye su kula da tarbiyyar ‘ya’yansu musamman ta hanyar tsawatarwa da kuma basu ilimi da tarbiyya ta hanyar nunawa kakanin nasu suna da mahimmaci

Sunana Musbahu Muhammad Gorondutse Kano:

Jikoki
Musbahu Muhammad

Wannan ba karamar Matsala ba ce, saboda tarbiyyar yaro wani lokacin dole sai an hada da duka, hana dukan zai iya haifar da lalacewar tarbiyyar ‘ya’yan. Babu riba kwata-kwata a hana bawa yaro cikakkiyar kulawa. Kwarai da gaske idan yaro ya tashi ba a kwabarsa zai Iya lalacewa ta fuskoki da dama kamar; Shaye-shaye, Sace-sace, Neman Mata, Fadace-fadace da sauransu. Iyayen yara su kula ba a kowanne laifi ake dukan yaro ba. Masu hana dukan su sani cewa ana dukan ne dan yaro ya gane yayi laifi, kuma su kansu iyayen da suke dukan ba dan su ji dadi suke yi ba, sai dan su ga yaro ya zama na gari me jin magana.

Sunana Mustapha Abdullah Abubakar daga Jihar Jos:

Jikoki
Mustapha Abdullah

Da farko dai a nawa fahimtar sirikan da  ba sa son a dakar musu jikokinsu ko da kuwa iyayen yaran ne, abin da ke saka hakan shi ne; Akwai shakuwa mai karfi ne tsakaninsu  da  jikokinsu, wanda matukar ana dukan jikokinsu sukan ji ba dadi, ko da kuwa iyayen yaran ne. A wani bangare kuwa, tun kafin Aure akan samu rashin fahimta tsakanin, uwar Ango da ita kanta Amaryan, wanda kan iya haifar da sirika ta tsani mahaifiyar yaro ko yarinyar, ta hanyoyi da dama. Wani lokacin sirikan kan fake da hakan ne domin tunzura uban yaro ya sake yin Aure, sabida rashin jituwar su. A Gaskiya babu wata riba ga duk sirikar da za ta saka danta sakin matarsa, ko kuma karo aure. Sabida wani dalili matukar ana so aci ribar aure. Akasin hakan ka sa ita uwar yaron daina ganin girman mahaifiyar mijin nata, akansin haka kuma kan haifar da munmunar matsala da rashin fahimta ko kuma kiyayya tsakanin bangarori guda biyu wato dangin Ango da kuma dangi Amarya. Hakan Kan haifar da daina ganin girman juna, kan haifar da daina bin umarnin sirikai, kan haifar da musayan kalamai maras dadi tsakanin juna. Shawara ga surikai masu aikata  irin wannan su ji tsoran Allah, su sani cewa wanna ba addini bane, son zuciya ne, da kuma bin hanyar halaka. Domin ko bayan mutuwar su, su kan tafi su bar mummunar tsana, ko rashin fahimta ga ‘ya’yansu. Iyayen yaro kuwa su yi koyi da  kyawawan halayya kamar; hakuri, da juriya, da nuna biyayya ga zaman aure, domin suna bin umarnin fiyayan halitta ne wato Annabi Muhammad (S.A.W), mutukar suka yi hakan ba shakka sakamakonsu na da girma a wajan Allah subhanahu wata’ala.

Sunana Amina Mu’awuya Mukhtar:

Jikoki
Amina Mu’awuya Muktar

Gaskiya hakan ba karamin babban kuskure ba ne, sabida hakan ya kan haifar da babbar  matsala ga tarbiyyar  yara, domin kuwa za su taso ba sa ganin darajarar iyayen su, za su taso a fandare ba sa ganin daraja da girmama duk wani na gaba da su, sabida tun farko sun gina su akan rashin ganin daraja da kimar iyayen su, duk wanda kuwa ya taso akan wannan turba to tabbas! ko ya girma a haka zai gina rayuwar shi, dan haka wannan babbar matsala ce. Hakan ba shida wata riba, domin kuwa ruguza   tarbiyya ne, akasin hakan kuwa shi ne gaba daya iyalan mutum za su ta so cikin rashin samun nagartacciyar tarbiyya. Tabbas! yana haifar da tarin matsaloli ba kadan ba. Rashin ganin darajar iyayen da suka haifi mutum, Gurbacewar tarbiyyar zuri’a. Shawarar da zan basu shi ne; ya kamata su gane cewa abin da suke ba dai-dai bane ko a cikin addinin musulunci, domin kuwa Manzon (s.a.w) ya ce; “Yardar Allah tana tare da Yardar iyaye, haka fushin Allah yana tare da fushin iyaye”, to ko dan wannan zan ce daga bakin mai gaskiya ya kamata ace Mutane mu hankalta mu bar jikokinmu su yi wa iyayen su biyayya, matukar biyayyar bata kaucewa umarnin Allah da Manzon sa ba, Allah ya sa mu dace.

Sunana Abdullahi Dahiru Matazu daga Jihar Katsina:

Jikoki
Abdullahi Dahiru Matazu

A Gaskiya wannan ba karamar matsala ba ce, domin idan muka yi duba da wasu abubuwan irin su; rashin ji na yaro, da kuma rashin yin sallah, wannan duk laifi ne da bai kamata a kyale yaro ba, dole a hukunta shi. Saboda haihuwar sa aka yi ba daga sama ya fado ba, kuma wannan ya tabbatar da cewa su fa sun tsufa babu abun da suke so illa yaran nan, saboda suna abokansu, kwakwalwar su iri daya ce. Babu wata riba sai ma faduwa, zai iya haifar da babbar matsala, kana zaune da matar ka lafiya an ce ka saketa, ka auro wata wacce baka san halinta ba. Kome iyayenmu za su yi mana ka da mu ji haushi, saboda su ne tsatson da aka samo mu jikinsu, mu yi ta hakuri da addu’a har Allah ya sa mu rabu lafiya.

Sunana Abubakar Muhammad Shehu daga Jihar Kano:

Jikoki
Abubakar Muhammad Shehu

Gaskiya hakan ba daidai bane, sakamakon hakan zai iya sa yaro ya zama ba shi da cikakkiyar tarbiyya, kuma baya ganin girman iyayansa. Yin hakan ba shi da wata riba, face rabuwar kai tsakanin ‘ya’ya da iyayan su, zai haifar da rashin ganin darajar iyayaye, sanan zai sa yaro ya gangare ya zama ba ya jin maganar kowa. Shawarata a nan ita ce; masu yin irin wannan ita ce su guji bata tarbiyyar jikokinsu, saboda gudun abin da zai je ya zo. Na gode, ina yi wa kowa fatan alkhairi.

Sunana Aisha Umar Kano:

Jikoki
Aisha Umar

Toh! gaskiya sirikan suna tunanin so ne suke nuna wa jikokin ba su san suna hallakar da rayuwarsu ba, ne Musamman idan suka sa aka saki iyayen yaran, ta nan ne yaran za su tashi ba tarbiyya, ba su ganin kimar kowa sun raina kowa saboda tun farko ba a tsawata musu ba.

Sunana Mas’ud Saleh Dokadawa:

Jikoki
Mas’ud Saleh Dokatawa

Gaskiya hakan yana faruwa kuma wannan ba ita ce mafita ba, ya kamata kakanni su rinka sawa zuciyarsu hakuri akan kananun abubuwa irin wannan. Sannan su ma iyaye mata su yarda cewa duka ba shi ne mafita ba ga tarbiyyar yara, addu’a da nasiha da tsawatarwa ita ce mafita. Ba shi da wani riba ko alfanu, karshe ma ya kawo rabuwar aure ko rusa zamantakewa me dadi, on haka kawar da kai ya fi komai a garesu. Matsalolin sun hada da Rashin ganin girman surukan, saboda sawa a sake su. Yawaita mutuwar aure, Sawa jikoki su raina kakanninsu mata saboda sawa a saki iyayensu da suke yi. Shawara ita ce; Iyaye su rinka yin abin da za su gyara zamantakewar ‘ya’yansu, ba lalatawa ba. Iyaye mata su rage dukan kananan yara a matakin horo, kakanni su daina shiga lamarin ‘ya’ya da jikokinsu dan hakan na janyo raini da rashin zamantakewa.

Jikoki
Rabi'at Sidi Bala
+ postsBio
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Fim ɗin ƙaddara: Anya Ana Samun Irin Wannan ƙaddarar Kuwa?
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Ko Kafa Ƴansandan Jihohi Zai Taimaka Wajen Kawo Ƙarshen Matsalolin Tsaro?
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Dalilan Da Suka Jawo Aka Ƙi Yin Maraba Da FIM House A Jihar Kano
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Zan Iya Auren Namiji Komai Talaucinsa Muddin Muna Son Junanmu -Maryam Labarina

MASU ALAKA

Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya
Taskira

Ra’ayin Al’umma Game Da Shirin Gwamnati Na Sake Fasalin Hukumar NYSC

July 11, 2026
Ko Kafa Ƴansandan Jihohi Zai Taimaka Wajen Kawo Ƙarshen Matsalolin Tsaro?
Taskira

Ko Kafa Ƴansandan Jihohi Zai Taimaka Wajen Kawo Ƙarshen Matsalolin Tsaro?

July 5, 2026
Bukatar Rike Sirri A Tsakanin Ma’aurata
Taskira

Bukatar Rike Sirri A Tsakanin Ma’aurata

June 13, 2026
Next Post
Sheikh Ibrahim Inyass

Yadda Daruruwan Dubban Jama'a Suka Halarci Maulidin Sheikh Ibrahim Inyass Karo Na 37

LABARAI MASU NASABA

Tinubu Yana Zuba Kyawawan Ayyuka A Nijeriya – Ganduje

Ganduje Ya Buƙaci A Yi Siyasar Aƙida Domin Inganta Dimokuraɗiyya A Nijeriya

July 16, 2026
Binciken CGTN: Amfanar Da Kowa Da Kowa Shi Ne Ainihin Alherin Da Fasahohin Kwaikwayon Tunanin Bil Adama Suka Kawo

Binciken CGTN: Amfanar Da Kowa Da Kowa Shi Ne Ainihin Alherin Da Fasahohin Kwaikwayon Tunanin Bil Adama Suka Kawo

July 15, 2026
Sin Ta Yi Kira Da A Kafa Tsarin Jagorantar Muhimman Ma’adinai Ga Sauyawa Zuwa Amfani Da Makamashi Mai Tsafta

Sin Ta Yi Kira Da A Kafa Tsarin Jagorantar Muhimman Ma’adinai Ga Sauyawa Zuwa Amfani Da Makamashi Mai Tsafta

July 15, 2026
Gwamna Dauda Lawal Zai Gabatar Da Jawabi A Taron Ƙasa Da Ƙasa Na Jami’ar FUE Zariya

Gwamna Dauda Lawal Zai Gabatar Da Jawabi A Taron Ƙasa Da Ƙasa Na Jami’ar FUE Zariya

July 15, 2026
Neman Raba-Gari Da Sauran Kasashe Zai Kawo Mummuann Tasiri Ga Bangarorin Da Abin Ya Shafa

Neman Raba-Gari Da Sauran Kasashe Zai Kawo Mummuann Tasiri Ga Bangarorin Da Abin Ya Shafa

July 15, 2026
Kevin Kelly: AI Na Iya Taimakawa Wajen Cimma Burin “Koyar Da Dalibai Da Kwazonsu”

Kevin Kelly: AI Na Iya Taimakawa Wajen Cimma Burin “Koyar Da Dalibai Da Kwazonsu”

July 15, 2026
Gwamna Yusuf Ya Bai Wa Masu Kula Da Akwatinan Zaɓe Na APC Filaye 1,540 Da Tallafin Miliyan 100

Gwamna Yusuf Ya Bai Wa Masu Kula Da Akwatinan Zaɓe Na APC Filaye 1,540 Da Tallafin Miliyan 100

July 15, 2026
Sabbin Ministoci

Rashin Tsaro: Majalisar Dattawa Ta Bukaci A Tura Ƙarin Sojoji da ’Yansanda Zuwa Benuwe

July 15, 2026
GDPn Sin A Rabin Farko Na Shekarar 2026 Ya Karu Da Kashi 4.7% Idan Aka Kwatanta Da Na Kwatankwacin Lokacin Bara

GDPn Sin A Rabin Farko Na Shekarar 2026 Ya Karu Da Kashi 4.7% Idan Aka Kwatanta Da Na Kwatankwacin Lokacin Bara

July 15, 2026
‘Yansanda Sun Tsaurara Tsaron Iyakokin Kano Bayan Hare-haren ‘Yan Bindiga 

Atiku Ya Nuna Damuwa Kan Kasafin Naira Biliyan 6.44 Don Gasar Cin Kofin Duniya ta 2026

July 15, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.