Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, ta zura kwallaye har biyar rigis a wasan farko na gasar UEFA Champions League ta bana da suka kara da Royal Antwerp a ranar Talata.
Kwallon wadda aka buga a filin wasa na Olympics Companys dake birnin Barcelona, an tashi ba tareda abokiyar karawar ta zura kwallo ko daya ba.
Sabon dan wasan aro na Barcelona Joao Felix ne ya fara zura kwallo a minti ashirin kacal da fara wasan, Lewondwski ya zura ta biyu kafin Batelle ya ci gida.
Bayan dawowa hutun rabin lokaci ne matashin dan wasa Gavi ya zura kwallonsa ta farko a gasar UEFA Champions League kafin Felix ya kara kwallo ta biyu a wasan.