Hukumar kulawa da lafiya matakin farko ta kasa ta bayyana cewa Nijeriya ta samu karin mutane 836 wadanda suka kamu da cutar a kananan hukumomi 33 daga Jihohi takwas da kuma Babban birnin tarayya FCT daga watan Mayu zuwa Yuli na wannan shekara 2023, ta kara jaddada cewar dukkan mutane 83 da aka tabbatar da kamuwa da cutar sun mutu.
Babban jami’i kuma shugaban hukumar kulka da lafiya matakin farko ta kasa NPHCDA,Dakta Faisal Shuaib,shi ya bayyana haka a taron manema labarai ranar Litinin ta makon da ake ciki dangane da barkewar cutar diphtheria a Nijeriya.
- Ana Ci Gaba Da Nuna Damuwa Kan Watsi Da Aikin Tashar Baro
- Wasu Hukumomin Kasar Sin Sun Ware Miliyoyin Kudi Domin Tallafawa Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa
Ya ce al’amarin da akwai tana hankali da ban tsoro na yadda al’amarin barkewar cutar diphtheria yake a Nijeriya daga watan Mayi zuwa Yuli 2023 an samu 2,455 da ake kyautata zaton sun kamu da cutar daga Jihohi 26. Sai dai kuma daga ranar28 ga Yuli 2023 bayan an yi gwaji an tabbatar da 836 ne suka kamu a kananan hukumomi 33 a Jihohi 8 da suka hada dacases: Kuros Ribas, Kano, Katsina, Kaduna, Legas, Osun, Yobe da Babban birnin tarayya FCT.
“An samu mutuwar 83 daga wadanda aka tabbatar da sun kamu da cutar abinda ya sa yana da matukar muhimmanci ayi ma ‘ya’yanmu da suke yara allurar rigakafi daga kamuwa daga cutar da take saurin kisa
Faisal ua bayyana cutar diphtheria a matsayin wadda za a iya kamuwa da ita ba makawa kamar yadda za a iya warkewa daga ita,wadda kwatar cutar bacterium Corynebacterium ta ke sanadiyar a kamu da ita, ta hanyar cudanya kai tsaye da wanda ya kamu da ita ko wani abin da ya zuba ta iska.
Ya kara bayanin kowa na iya kamuwa da cutar bama kamar kananan yara.
“Sai dai kash! kamar yadda ya furta abin tada hankali har yanzu akwai yaran da ba ayi ma allurar rigakafi ba duk kuwa da yake akwai alluran kamar yadda aka tanada a Nijeriya,kamar yadda Faisal ya tabbatar.
Cutar Diphtheria tana shafar wuraren da su ke taimakawa wajen shakar numfashi, alamun ta sun hada da zazzabi,Tari zubar wani abu daga Hanci, ciwon mashako, kumbirin wuya,da samun matsala wajen yin numfashi.
Ya ce idan ba a dauki matakin samar da magani ba alamun da aka gani na iya sanadiyar mutuwa, musamman ma idan aka ce ba ayi wa allurar rigakafin data dace ba, ko ma gaba daya ba ayi ba,a wurin da babu tsafta ko inda ake da cunkosa al’umma.
Babban jami’in ya ce, cutar ana iya maganinta ta hanyar allurar rigakafi.
Kamar yadda ya kara jaddadawa a Nijeriya ana yin amfani da alluran,pentabalent a matsayin kariya daga kamuwa da cutar diphtheria ana yi ma yara daga mako 6,mako 10, mako 14 tare da karin wasu allurai lokacin da ake shiri na wayar da kai.
Ya yi karin haske na cewa “Duk da kokarin da gwamnatin tarayya ta keyi na samar da alluran da basu da tsada akwai yaran da har yanzu ba a samu damar yi masu allurar ba, ko kuma an yi masu amma bata isa kamar yadda ya dace ba, irin hakan ke kawo koma bayan duk wani kokarin da kasa ta ke yi, na samar da kariya. Rashin samun allurar rigakafi ta Suboptimal duk ita ce babbar matsalar da ke taimakawa ga yawan barkewar cutar inda al’amarin ke shafar yara daga shekara biyu (2) zuwa goma sha hudu(14).