Mun samu Labarin Rasuwar Ciritawan Zazzau, Alhaji Isyaku Muhammad Ashiru Mai Shekaru 92 bayan ya yi fama da doguwar jinya.
Wata Sanarwa daga Wakilin Yada labaran Masarautar Kudan, Yusuf Ibrahim kudan, ta ce Alhaji Isyaku Muhammad Ashiru kafin rasuwarsa ya taba zama Hakimin Kudan a yankin karamar hukumar Kudan a cikin Jihar Kaduna.
Marigayin ya rasu ya bar mata 3 da ‘ya’ya 24 da jikoki da dama da kuma ‘yan uwa maza da mata. Cikin su akwai Mayanan Arewan Zazzau kuma Hakimin Hunkuyi Aminu Muhammad Ashiru sai Alhaji Isa Muhammad Ashiru, ɗan takarar Gwamnan Jihar Kaduna a zaben shekarar 2023, Isah Ashiru da wasu da dama.
Tuni dai aka yi jana’izarsa fadar Hakimib Kudan.