Bankin Raya Afirka, ya amincewa Gwamnatin Tarayya wani sabon bashin na dala miliyan 500.
Sabon bashin, ya nuna yadda Bankin ya bai wa ƙasar bashin da ya kai jimlar dala biliyan 5.1 tun daga ranar 31 na watan Okutobar 2025.
Kazalika, wannan sabon bashin, zai taimaka wa kashi na biyu na shirin haɓaka tattalin arzikin samar da makamashi da kuma samar da sauye-sauye, a fannin na makamashin da cimma burin da ake dashi, na rage ɗumamar yanayi.
A cikin sanarwar da jami’in samar da bayanai da hulɗa da jama’a na ƙere na Bankin Aleɗis Adélé ya fitar ya sanar da cewa, daraktocin Bankin, biyo bayan wata ganawa da suka yi a birnin Abidjan sun amince da a bai wa Nijeriya wannan bashin.
- Za A Bude Shafin Karbar Bashin Dalibai A Ranar 24 Ga Mayu
- Amurka Za Ta Ƙaƙabawa Wasu ‘Yan Nijeriya Takunkumi
Sanarwar ta ce, bashin ya fara ne daga 2024 zuwa 2025, wanda kuma zai ƙara ƙarfafa kashi na biyu na shirin.
A zagaye na farko na shiri, za a ƙara ƙarfafa sauye-sauye wajen tafiyar da kuɗaɗe da tabbatar da ana bin ƙa’ida da kuma sanya ido, kan yadda ake kashe kuɗaɗen Gwamnati.
Bugu da ƙari a zagaye na biyu kuma, manufar shi ne, a ƙara haɓaka samar da makamashi da faɗaɗa samar da wutar lantarki wanda hakan zai bayar da dama, wajen janyo kamfanonin masu zaman kansu domin su zuba jari, a fannin.
A jawabinsa Darakta Janar na Bankin a Nijeriya Abdul Kamara, ya sanar da cewa, a zagaye na farko na shirin ya haɗa da samar da sauye-sauye a fannin makamashi, musamman bisa nufin haɓaka samar da kuɗaɗen shiga ga fannin da bai shafi Man Fetur ba.
Ya ƙara da cewa, shirn zai kuma tallafa wa sahiri na ƙasa na NDC wanda zai fara aiki daga 2026 zuwa 2030, musamman duba da cewa, shirin yayi daidai da ƙoƙarin da ake yin a yaƙar sauyin yanayi.
Bisa wasu ayyuka guda 52 wanda rancen kuɗin ya kai dala biliyan to 5.1 inda ƙarin wannan ranncen zai ƙara bunƙasa tattalin arzikin ƙasar nan, musamman ta ɓangaren samar da sauye-sauye.
Sauran rancen da Bankin ya bai wa Nijeriya a baya sun haɗa da, wanda aka bayar a watan Yuli wanda ya kai dala miliyan 500 daidai da Naira biliyan 766.7.
Hakazali,a akwai kuma wani rancen da aka bayar a watan Mayu wanda ya kai dala miliyan 650 daga 2025 zuwa 2030.














