Wasu ɓata gari sun daka wa wata motar dakon kayan abinci ta Kamfanin BUA wawa a unguwar Dogarawa da ke babban titin Zariya zuwa Jihar Kano.
Ɓata garin dai kamar yadda ganau ya shaida wa wakilinmu cewa sun dauke katon-kato na taliya da motar ke ɗauke da su a da yammacin Juma’a.
- An Rage Hukuncin Kwashe Maki 10 Da Aka Yi Wa Everton
- Talauci Da Rashin Aikin Yi Ne Silar Matsalar Tsaro A Arewa – Dan Masani
Ɓata garin sun kai wa motar hari ne da misalin karfe 3 na rana lokacin da direban motar ya tafi kama ruwa don yin ibada.
Wani ganau ya shaida wa LEADERSHIP Hausa cewa, direban ya tsaya ne don kama ruwa don yin Sallah.
Nan take, suka gane cewa taliya ce a cikin motar suka afka mata tare da wawashe duk abin da suka ci garo da shi a cikin motar.
Ganau din ya kara da cewa ɓata garin sai da suka wawushe dukkan katan-katan ɗin taliyar da motar ke ɗauke da shi kafin daga bisani kowa ya tsere da abin da ya samu gida.
Wakilinmu ya ruwaito cewa daga baya dai jami’an tsaro sun kawo dauki domin ɗaukar matakin gaggawa
Ya zuwa hada wannan labarin dai jami’an tsaro yankin sun cika hannu da wasu daga cikin bata garin.
Amma an tafka asara mai yawa.