Shugaban jam’iyyar AA, Kenneth Udeze, ya yi watsi da rahotannin kafafen yada labarai na cewa, wata kotu ta bayar da umarnin kama tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, tare da ɗaure shi.
Udeze, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, ya bayyana rahotannin a matsayin ƙarya kuma ya bukaci ‘yan Nijeriya da su yi watsi da su.
- Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Kan Saɓa Umarninta
- Adadin Biyan Kudade Ta Intanet Yayin Hutun Bikin Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin Ya Kai Yuan Tiriliyan 13.26
A baya dai an samu rahoton cewa mai shari’a Adefunmilola Demi-Ajayi na babbar kotun tarayya da ke zamanta a garin Osogbo na jihar Osun, ya bayar da umarnin tsare Farfesa Yakubu tare da daure shi bisa zargin kin bin hukuncin da kotu ta yanke dangane da karar da wasu tsofaffin ‘ya’yan jam’iyyar AA suka shigar.
Rahotanni sun bayyana cewa, karar mai lamba FHC/OS/194/2024, ta nemi umarnin tilastawa INEC da shugabanta na lokacin da su sanya sunayen wasu jami’an Jam’iyyar AA a shafin hukumar na yanar gizo bayan an cire su.
Sai dai Udeze ya ci gaba da cewa, babu irin wannan hukunci ko umarnin kama shi (Yakubu), yana mai tabbatar da cewa, rahotannin ƙage ne kawai.