Wata Baturiya wacce aka danganta cewa ta fi kowa tsofa a duniya, mai suna Maria Branyas wadda aka haife a ranar 4 ga watan Maris a shekarar 1907, a San Francisco da ke Jihar California ta kasar Amurka, ta mutu tana da shekaru 117.
Maria ta mutu ne a ranar Litinin bayan ta shafe karnin biyu na rayuwarta a Santa Maria del Tura da ke a yanin Olot a arewacin Catalonia ta kasar Amurka.
- Mutum Miliyan 7.9 Da Ta’addanci Ya Tagayyara A Jihohi 3 Na Bukatar Agaji – UNOCHA
- Takaitaccen Nazari A Kan Noman Nau’o’in Abinci 7
Mariya Branyas dai ta ga karni da bama da suka gabata wanda kuma a gaban idonta ne aka gudanar da wasu manyan tarukan tarihi.
A watan da ya gabata, Maria ta zamo ta takwas wajen kafa tarihi wanda har aka sanya sunanta a cikin kudin bincike na GRG, wanda kudin tarihi da ake kira a Turance na ‘Guinness World Records’, ya sanya sunanta a cikin jerin mutanne da suka shafe tsawon shekaru a duniya.
A ranar 17 ga watan Janairun shekarar 2023, Maria ta samu kambun zama wadda ta shafe shekaru a duniya bayan mutuwar wani dan kasar Faransa mai suna Lucile Randon, wanda ya mutu yana da shekaru 118.
Kazalika, a lokacin tana ‘yar shekara bakwai aka yi yakin duniya na shekarar 1914, mahaifiyarta, ta yanke shawarar koma wa Catalonia da sauran iyalanta.
Mariganya Maria, a wata hira da aka yi da ita a shekarar 2019, ta iya tunano yadda ita da mahifiyarta da sauran ‘yanuwanta suka ratsa Kogin Atlantic a cikin jirin kwale-kwale, saboda yakin ya sa kasar Gamus ta kasance tana ci gaba da kai farmaki a yankin arewa, wanda hakan ya sanya suka gaza yin wani nisa zuwa kasar Cuba.
A yayin hirar da ake yi da ita wadda take yin magana a hankali, amma bakinta garau, ta ce, “A shekarar 1914 na kasance ina sane da ‘yan abubuwan da suka gudana”.
Maria duk da wadannan shekarun da ta shafe a duniya, ta kuma iya tuna yaka-yakan duniya da kuma na kasar Safaniya.
Duk a cikin hirar, ta kuma yi bayani radadin yakin na Sifaniya, wanda aka yi daga shekarar 1936 zuwa 1939, inda ta bayyana cewa, “Na tuna abubuwa marasa dadi game da yakin wanda a wancan lokacin wasu mutane suka rinka aikata mummunar ta’asa kuma ba wanda zai iya ce masu uffan”.
A cikin watan Mayun 2020, a lokacin tana da shekara 113, Maria ta kasance tsohowar da ta tsallake siradin annobar cutar Korona, wanda hakan ya kara daga kimarta.
Saboda tsawon shekarun da ta shafe, hukumar masu sanya ido ta San Francisco, a hukumance ta karrama Maria a shekarar 2023, bayan ta cika shekara 116 da kwanuka 249 a duniya.
Bugu da kari, hukumar ta kuma ware duk ranar 7 na watan Nuwamba a matsayin ranar Maria a San Francisco.