Wata tawagar haɗin gwuiwa daga jihohin Bauchi da Gombe ta nuna damuwa matuƙa kan jinkirin da ake samu a aikin ci gaban haƙar mai na Kolmani, wani babban shiri da aka fara a kan iyakar jihohin biyu.
Tawagar wadda ta ƙunshi Kwamishinan Raya Albarkatun Ƙasa na Jihar Bauchi, Muhammad Maiwada Bello, da Kwamishinan Ma’aikatar Albarkatun Ƙasa na Jihar Gombe, Sunusi Ahmad Pindiga, sun bayyana matsayinsu ne yayin da suka kai ziyara ta musamman zuwa ramin haƙar man da ke Kolmani.
- Kwamitin Ɗanyen Mai Ya Nuna Rashin Gamsuwa Da Jinkirin Haƙo Mai A Kolmani
- Bayan Wata 16 Da Kaddamarwa: Gwamnati Ta Dakatar Da Hakar Man Kolmani
A yayin ziyarar, sun bayyana rashin jin daɗinsu kan yadda aikin ke tafiya a hankali, inda suka buƙaci kamfanin da ke da alhakin aikin da ya gabatar da cikakken bayani game da matsayin aikin da kuma lokacin da za a kammala.
Kwamishina Bello ya ce, “Wannan aiki yana da matuƙar muhimmanci ga tattalin arziƙin jihohinmu biyu. Jinkirin da ake samu yana rage wa al’umma burin da suke da shi. Dole ne mu shiga tsakani domin a gaggauta aiwatar da abubuwan da suka dace.”
Shi ma a nasa jawabin, Kwamishina Pindiga ya jaddada buƙatar bayyananniyar mu’amala da gaskiya daga masu aikin. “Wannan aikin tarihi ne ga yankin Arewa maso Gabas. Ba za mu amince a mayar da shi saniyar ware ba saboda rashin tsari ko sakacin aiki.”
Tawagar ta ƙunshi kwamishinoni, da sakatarorin dindindin, da daraktocin albarkatun man fetur da kuma manyan shugabannin gargajiya daga jihohin biyu, wanda hakan ya nuna muhimmancin aikin da kuma haɗin kan da ake nema domin ganin ya cimma nasara.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp