A ranar Talata ce, gwamnatin Jihar Bauchi ta sanar da mika ragamar filin jirgin sauka da tashi na Sir Abubakar Tafawa Balewa ga hukumar kula da filayen jiragen sama ta Nijeriya (FAAN), domin kyautata kula da shi da bunkasar tattalin arzikin jihar.
Da yake ganawa da ‘yan jarida jim kadan bayan mika ragamar filin jirgin a Bauchi, mataimakin gwamnan jihar, Muhammad Auwal Jatau, ya ce, an kammala cika sharadun da suka dace, yanzu haka komai da komai na filin jirgin ya koma karkashin gwamnatin tarayya.
- Ministan Sufuri Ya Nada Sabon Manajan Gudanarwa Na FAAN, Yayin Da Wa’adin Yadudu Ya Kare
- ‘Yansanda Sun Hallaka Ɗan Garkuwa Da Mutane, Sun Ceto Mutun 6 A Bauchi
Jatau, wanda ya amshi tawagar FAAN a madadin gwamnan jihar, Bala Muhammad, ya nuna kwarin guiwarsa da cewa, bisa wannan mika ragamar filin jirgin saman jihar da ma shiyyar arewa maso gabas za su kara samun bunkasar ci gaba.
Shi kuma a nasa bangaren, daraktan gudanarwa na hukumar FAAN, Kabir Yusuf Muhammad, ya ce majalisar zartaswar gwamnatin tarayya ta amince da wasu maguden kudade da za a mayar wa gwamnatin Jihar Bauchi sakamakon amsar filin jirgin.