Bayan karbar makudan kudade a matsayin kudin fansa, wani kasurgumin dan fashin nan mai suna Dogo Daji, ya saki hudu daga cikin dalibai 11 da suka yi garkuwa da su a Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya da ke Yauri, Jihar Kebbi.
An tattaro cewa biyu daga cikin daliban da aka sako sun dawo da jarirai biyu a hannunsu.
- Yadda Manyan Jam’iyyu Suka Fada Cikin Rikici Bayan Zabe
- Jerin ‘Yan Wasan Kungiya Daya Da Suka Yi Fada Da Juna
Dogo Daji ya jaddada cewa sai an cika wasu sharuda da gwamnatin Jihar Kebbi kafin a sako sauran ‘yan matan.
Majiyoyi sun kara da cewa dole ne iyaye da sauran masu ruwa da tsaki su samar da kudin fansa a lokacin da gwamnatin Jihar Kebbi ta ki biyan bukatun ‘yan bindigar.
Sai da iyayen daliban sun roki ‘yan Nijeriya da su kawo musu agajin kudi domin ceto ‘ya’yansu daga hannun wadanda suka sace su.
A cikin wata wasika da ta aike wa daukacin ‘yan Nijeriya a watan Janairun 2023, wadda Leadership Hausa ta samu, kungiyar da aka fi sani da “Kwamitin Iyayen dalibai 11 da aka sace na F.G.C Birnin Yauri, Jihar Kebbi, Nijeriya,” ta bukaci taimakon kudi domin tara zunzurutun kudi har Naira miliyan 100 a matsayin kudin fansa da za a biya ‘yan ta’adda.
A cikin wasikar, shugaban kwamitin iyayen, Salim Ka’oje da kuma Mista Daniel Alkali, sun ce ‘ya’yansu mata sun kasance a hannun wadanda suka sace su kusan watanni 20 kawo yanzu.
“…Kuma wadanda suka sace ‘yan matan suna neman Naira miliyan 100 kafin su sako su,” in ji su.
Idan za a iya tunawa, an yi garkuwa da daliban mata 11 ne a lokacin da ‘yan bindiga suka kai hari makarantarsu a ranar 17 ga watan Yuni 2021.
A watan Nuwamban shekarar da ta gabata ne aka ruwaito cewa wasu daga cikin ‘yan matan sun haihu, yayin da wasu kimanin hudu ke dauke da juna biyu a lokacin.