ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, November 12, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Bayan Cin Kamfanin META Tarar Dala Miliyan 220: Sun Yi Bazaranar Katse Kafofin Facebook, WhatsApp, Da Instagram A Nijeriya

by Sani Anwar
6 months ago
Facebook

Kamfanin da ya mallaki shafukan Facebook, Instagram da kuma WhatsApp (Meta), ya yi gargadin cewa; za a iya tilasta masa rufe shafukan nasa a Nijeriya, sakamakon karuwar matsin lamba da kuma dimbin tara da gwamnati ta lafta masa, wadda ya bayyana cewa, “ba abu ne mai yiwuwa ba”.

Gargadin ya fito ne ta hanyar shigar da kara koto da BBC ta samu, yayin da kamfanin Metan ke ci gaba da cin karo da tarar dala miliyan 220 da Hukumar Kula da Al’amuran Kasuwanci ta Nijeriya (FCCPC) ta ci tararsa, sakamakon zargin keta bayanan sirri.  

  • Yahoo: Facebook Ya Kulle Asusun ‘Yan Nijeriya 63,000 
  • Kamfanin Meta Ya Goge Shafin Facebook Na Mawaƙi Rarara

Tarar dai, ta biyo bayan binciken hadin gwiwa na tsawon wata 38 da Hukumar FCCPC da Hukumar Kare Bayanan Sirri ta Nijeriya (NDPC) suka yi, kan yadda ake tafiyar da bayanan kamfanin Meta da dandalinsa na WhatsApp.

ADVERTISEMENT

Duk da hukuncin ranar 25 ga Afrilu da kotu ta tabbatar da tarar, kamfanin na Meta ya sha alwashin daukaka kara. Kotun ta bai wa kamfanin har zuwa karshen watan Yuni, ya yi biyayya ga hukuncin.

A wajen shigar da karar, kamfanin na Meta ya yi nuni da cewa; don rage hadarin tilastawar, yana iya rufe shafukansa na Facebook da Instagram a Nijeriya. Amma kamfanin bai ambaci shafin WhatsApp a cikin takardar kotun ba.

LABARAI MASU NASABA

Bayan Ganawa Da Tinubu, COAS Ya Tabbatar Wa ‘Yan Nijeriya Samun Ingantaccen Tsaro

Cikin Wata Ɗaya, ‘Yansanda Sun Kama Mutane 200 Da Ake Zargi Da Laifuka A Katsina

BBC ta rawaito cewa, babban abin da ke damun kamfanin na Meta shi ne, yadda al’amarin ya shafi Hukumar Kare Bayanan Sirri ta Nijeriya (NDPC), wanda kamfanin ke zargin karya dokokin kare bayanan sirrin kasar.

Baya ga tarar Hukumar FCCPC, hukumar ta NDPC ta ci tarar kamfanin Meta dala miliyan 37.8, bisa zargin satar bayanan sirri, yayin da hukumar kula da tallace-tallace (ARCON) ta fitar da wani hukuncin daban na dala miliyan 37.5, kan abin da ta kira da cewa, tallan da ba a ba da damar aiwatar da shi ba.   

Daga cikin ka’idojin da ake da su, akwai bukatar kamfanin na Meta ya samu izini kafin tura bayanan ‘yan Nijeriya zuwa kasashen waje, yanayin da kamfanin ke ganin “ba abu ne mai yiwuwa ba.”

Hukumar NDPC ta kuma bai wa kamfanin Metar umarnin kirkira da kuma nuna abubuwan ilimantarwa a kan hadarin bayanan sirri ta kebabbiyar hanya a kan shafukan nata. Dole ne a samar da wadannan bidiyoyi tare da cibiyoyin da aka amince da su da kuma masu zaman kansu, sannan kuma dole ne su magance ayyukan sarrafa bayanai da rashin adalci.

Amma kamfanin na Meta ya ja baya a kan wadannan umarni, yana mai bayyana su a matsayin “wadanda ba sa aiki” tare da tabbatar da cewa; hukumomin Nijeriya sun gaza aiwatar da fassarar dokokin bayanan nasu yadda ya kamata.

Hukumar ta FCCPC ta ci gaba da cewa, tarar ta biyo bayan cikakken binciken da aka gudanar tsakanin watan Mayun 2021 zuwa Disambar 2023, tare da hadin gwiwar hukumar ta NDPC.

Har ila yau, kamar yadda rahotannin ke nunawa, akwai yiwuwar a wayi gari a ga dib, wadannan shafuka na Facebook da na Instagram sun daina aiki a Nijeriya, sakamakon wannan dimbin tara da kamfanin Metan ya koka a kai.

Idan za a iya tunawa, a bara ne hukumomin sanya ido na Nijeriya suka lafta wa kamfanin tara ta fiye da dala miliyan 290, bisa zargin kamfanin da karya wasu dokoki.

Kazalika, sai ga shi kuma kamfanin na Meta bai samu nasara a karar da ya shigar a wata babbar kotu da ke Abuja ba, inda ya kalubalanci matakin.

Har wa yau, kamfanin Meta ya rubuta a takardun shigar da karar da ya yi cewa;  “Za a iya tursasa wa mai shigar da kara rufe ayyukan shafukansa na Facebook da Instagram a Nijeriya, domin rage hatsarin da zai iya fadawa a ciki, idan bai bi umarnin da ya kamata ya bi ba.”

Bugu da kari kuma, kamfanin Meta ne ke da manhajar WhatsApp, duk da cewa dai kamfanin bai ambaci shafin na WhatsApp din ba a jerin bayanan nasa.

Duk da cewa, babbar kotun ta bai wa kamfanin wa’din zuwa karshen watan Yuni, domin biyan wannan tara, amma da aka tuntubi kamfanin na Meta kan matakin da zai dauka, bai ce ko uffan ba.

Wadane Tasiri Manhajojin Facebook, Instagram Da WhatsApp Ke Da Su Kan ‘Yan Nijeriya

Ganin yadda ‘yan Nijeriya suka rumgumi wadannan shafuka ko manhajoji (Facebook, Instagram da WhatsApp), wasu suke ganin ba karamin nakasu za a samu ba, idan wannan kamfani na Meta ya janye daga Nijeriya.

Facebook ne shafin da al’umma suka fi amfani da shi a Nijeriya, domin kuwa miliyoyin al’ummar kasar ke amfani da shi a kowace rana. Wannan dalili, ya zama kusan na komai da ruwanka, kama daga abubuwan da suka shafi tallata hajoji, samun kowane labaru da dumi-duminsu da sauran makamantansu.

Har ila yau, shafin Facebook ya zama wata matattara ko dandali da ‘yan siyasa ke amfani da shi, musamman wajen yada farfagandar siyasa ko tallata manufofinsu ko kuma ayyuka da suka gudanar.

Kazalika, hatta kafofin yada labarai na amfani da wannan manhaja, wajen bayyana labaru da sauran shirye-shiryen da suke gudanarwa na yau da kullum.

A bangaren kasuwanci kuwa, wannan shafi ya shahara kwarai da gaske, domin kuwa kamfanoni da sauran ‘yan kasuwa; na amfani da shi, domin tallata hajojinsu iri daban-daban. Hatta masu shirya fina-finai, su ma ba a bar su a baya ba, domin kuwa sukan dan gutsuro wani abu daga ciki su nuna, don jan hankalin masu kallo.

Haka zalika, bangaren manhajar WhatsApp, ita ma na da nata matukar muhimmancin, musamman ta fuskar kasuwanci, sada zumunta, fadakarwa, ilimantarwa, tura wasu sakwanni masu muhimmanci da sauran makamantansu.

Wannan manhaja ta Whatsapp, kusan an fi amfani da ita wajen gudanar da kasuwanci, musamman ga daidaikun ‘yan kasuwa masu tasowa, har ma da wadanda wuyansu ya yi kauri.

Babban abin sha’awar shi ne, mata da dama daga gidajensu; na aiwatar da sana’o’i iri daban-daban, ta hanyar amfani da wannan manhaja, suna tallatawa ana kuma saya daga inda suke; ba tare da wata wahala ko kai-komo ba.

Haka nan, ga wadanda suke da ‘yan’uwa da sauran abokan arziki a kasashen ketare, wannan manhaja ta Whatsapp na matukar taimaka musu ta hanyar magana ko bidiyo kai tsaye a tsakaninsu, maimakon magudan kudaden da za su batar ta hanyar amfani da kiran waya.

Sannan uwa-uba, shafin Whatsapp; na da matukar muhimmanci wajen tura sakwannin karatuttuka, jaridu, labaru, hotuna, bidiyo da kuma sakon magana a kowane lokaci.

Haka zalika, ita ma manhajar Instagram na da nata muhimmancin, wajen tura sakwanni, sada zumunta, bidiyo, tallata hajoji da sauran abubuwa masu muhimmanci.

Koda-yake, akwai abubuwa da dama da ake ganin cewa; wadannan manhajoji sun taimaka wajen gurbacewarsu, wanda ko shakka babu, haka abin yake; musamman a bangaren gurbacewar tarbiyya da sauran abubuwan da suka shafi aikata ta’addanci da sauran makamantansu.

Duk da cewa, manhajojin sun taimaka wajen wayar da kan al’umma ta fuskoki daban-daban da suka hada addini, siyasa da sauran al’amuran rayuwa na yau da kullum, amma fa akwai abubuwa da yawa da suka yi tasiri a kan al’ummar wannan kasa ta hanyar amfani da manhajojin.

Kafin zuwan shafukan na Facebook, Instagram da Whatsapp, matasa da dama ba su da hanyoyin kale-kallen bidiyo da sauran hotunan batsa, barkatai. Amma bayan fitowarsu, yanzu za a iya cewa; lamarin ya riga ya zama jiki a tsakanin matasanmu.

Sannan, akwai sauran ayyukan rashin gaskiya da ta’addanci da matasa ke gani, maimakon su wa’antu; sai su buge da koya suna aikatawa. Akwai abubuwan da suka shafi damfara, aikewa da labarun karya da farfaganda, domin neman abun duniya ko wata daukaka a tsakanin al’umma.

Amma duk da wadannan abubuwa da ke faruwa a tsakanin manhajojin, muna iya cewa; amfaninsu ya fi rashin amfaninsu yawa a tsakanin al’ummar wannan kasa.

Shi yasa muke ganin janyewar kamfanin Meta daga Nijeriya, ba karamin koma-baya zai kawo mana ba. Amma wannan ya rage ga mahukunta, wajen dubawa tare da aiwatar da abin da ya dace, tun kafin alakar ta yi tsami.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Coas
Manyan Labarai

Bayan Ganawa Da Tinubu, COAS Ya Tabbatar Wa ‘Yan Nijeriya Samun Ingantaccen Tsaro

November 11, 2025
Cikin Wata Ɗaya, ‘Yansanda Sun Kama Mutane 200 Da Ake Zargi Da Laifuka A Katsina
Manyan Labarai

Cikin Wata Ɗaya, ‘Yansanda Sun Kama Mutane 200 Da Ake Zargi Da Laifuka A Katsina

November 11, 2025
‘Yan Majalisa 60 Sun Yi Barazanar Ficewa Daga PDP
Manyan Labarai

Kotu Ta Sake Hana PDP Gudanar Da Babban Taronta Na Ƙasa

November 11, 2025
Next Post
Mambobin APC Sun Buƙaci EFCC Ta Sake Buɗe Binciken Matawalle

Mambobin APC Sun Buƙaci EFCC Ta Sake Buɗe Binciken Matawalle

LABARAI MASU NASABA

Coas

Bayan Ganawa Da Tinubu, COAS Ya Tabbatar Wa ‘Yan Nijeriya Samun Ingantaccen Tsaro

November 11, 2025
Sin: Amurka Ba Ta Sa Lura Ga Kare Hakkin Dan Adam

Sin: Amurka Ba Ta Sa Lura Ga Kare Hakkin Dan Adam

November 11, 2025
Bikin CIIE Ya Nuna Yadda Sin Ke Ba Da Jagora Kan Harkokin Bude Kofa

Bikin CIIE Ya Nuna Yadda Sin Ke Ba Da Jagora Kan Harkokin Bude Kofa

November 11, 2025
Za Mu Ci Gaba Da Tallafa Wa ’Yansanda Domin Inganta Ayyukan Su A Zamfara – Gwamna Lawal

Za Mu Ci Gaba Da Tallafa Wa ’Yansanda Domin Inganta Ayyukan Su A Zamfara – Gwamna Lawal

November 11, 2025
CIIE Ya Kasance Gadar Sada Tattalin Arzikin Kasar Sin Da Na Duniya

CIIE Ya Kasance Gadar Sada Tattalin Arzikin Kasar Sin Da Na Duniya

November 11, 2025
CMG Ya Gabatar Da Sabbin Manhajoji 10 Da Ya Kirkiro Don Watsa Gasar Wasannin Motsa Jiki Ta Kasar Sin Karo Na 15

CMG Ya Gabatar Da Sabbin Manhajoji 10 Da Ya Kirkiro Don Watsa Gasar Wasannin Motsa Jiki Ta Kasar Sin Karo Na 15

November 11, 2025
‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 3 A Nasarawa

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 3 A Nasarawa

November 11, 2025
Cikin Wata Ɗaya, ‘Yansanda Sun Kama Mutane 200 Da Ake Zargi Da Laifuka A Katsina

Cikin Wata Ɗaya, ‘Yansanda Sun Kama Mutane 200 Da Ake Zargi Da Laifuka A Katsina

November 11, 2025
CIIE Ya Ba ‘Yan Kasuwar Afirka Damar Habaka Cinikinsu Da Sin 

CIIE Ya Ba ‘Yan Kasuwar Afirka Damar Habaka Cinikinsu Da Sin 

November 11, 2025
Me Sabon Tarihin Da Aka Kafa A Baje Kolin CIIE Ke Nunawa?

Me Sabon Tarihin Da Aka Kafa A Baje Kolin CIIE Ke Nunawa?

November 11, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.