Hukumar Yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta gano Naira biliyan 80 a cikin asusun bankin wani daga cikin tsoffin daraktocin Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPCL) wanda aka sallama. Wannan ganowa na cikin wani bincike kan yadda aka yi amfani da kudaden $2.96 biliyan domin gyaran Matatar man fetur a Nijeriya.
A cikin wannan bincike, EFCC ta kama tsofaffin daraktocin kamfanonin man fetur guda uku, wato Matatar Man Fetur ta Port Harcourt (PHRC), Matatar Man Fetur ta Warri (WRPC), da Matatar Man Fetur ta Kaduna (KRPC), da kuma wasu manyan jami’an NNPCL. An gudanar da bincike kan yadda aka kashe kudade masu yawa na gyaran Matatun.
- Shugaban NPA Dantsoho Ya Bayyana Aniyar Inganta Ayyukan Hukumar A Wannan Shekarar
- Tinubu Ba Ya Tsoma Baki A Ayyukan EFCC – Olukoyede
EFCC tana binciken yadda aka saki kudaden daga gwamnati domin gyaran Matatatun man fetur, ciki har da $1,559,239,084.36 da aka kashe a Port Harcourt, $740,669,600 a Kaduna, da $656,963,938 a Warri, wanda jimillar su ta kai $2,956,872,622.36. Akwai tsoffin daraktoci da dama da aka kama ciki har da Ibrahim Onoja na PHRC da Efifia Chu na WRPC.
Binciken ya kuma shafi Mele Kyari, tsohon Shugaban Kamfanin Man Fetur na Kasa, da sauran manyan jami’an da aka jera a cikin wata takarda daga EFCC. Takardar ta nemi Kamfanin NNPCL ya bayar da cikakken bayani game da albashinsu da sauran alawus-alawus na jami’an da aka lissafa.
EFCC ta bayyana cewa binciken yana ci gaba da gano yadda aka sace kudaden gwamnati a cikin wannan tsari na gyaran Matatun man fetur, kuma tana matukar son ganin an dauki matakin doka kan wannan lamarin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp