Wani Ango a Unguwar Kundila da ke Jihar Kano da majiyarmu ba ta bayyana sunansa ba, ta ce an sace kayansa a kasa da awa 24 da daurin aurensa, wanda barayi suka fasa wurin da aka ajiye kayan suka yi awon gaba da shi.
Ango ya wayi gari babu suturar da ya tanada dan zuwa daurin aurensa na farko, wanda hakan ta faru a Unguwar Kundila Kano a cikin karamar hukumar Tarauni kamar yadda majiyar ta tabbatar mana da labarin wannan abu da ya faru a ranar Asabar da ta gabata.
- Yanzu Da Aka Fara Hako Mai A Arewa…
- Matan Tubabbun ‘Yan Boko Haram Sun Haifi Jarirai 262 A Wata 4 Kacal
Haka wani labarin kuma daga Unguwar Fagge, an sace kudin sadaki a taron daurin aure shi ma a ranar Asabar a karamar hukumar Fagge Jihar Kano. Sakamakon sace kudin sadakin da iyayen ango suka zo da shi, an daura auran ne ajalan ba lakadan ba, ba kamar yadda aka saba daura aure ba tare da bin bashin sadaki ba.
Matasa da sauran jama’ar Kano ci gaba da yin Allah-wadai da wannan sata ta rashin tausayi, inda suka bayyana ra’ayinsu da cewa sace sadaki da suturar shigar angonci wani sabon batanci ne da barna da ake so a shafa wa al’ummar jihar kashin kaji da shi.
Abdussalam wanda akafi sani da Mamu Kofar Nassarawa ya ce wannan abu darasi ne da ya kamata matasa su dauka wajen kula da sadaki duk lokacin da za a yi daurin aurensu domun kauce wa wannan ila ta rashin tausayi.
Shi ma wani matashi mai suna Usaini wanda aka fi sani da Malam Malam Unguwar ‘Yan Bita da bai yi auren fari ba, ya ce wannan labari ya girgiza shi sosai. Ya ce da yana da hali zai iya biya wa mai auren nan sadaki kuma da dinka wa ango kayan da aka sace don faranta musa rai.