Jami’ar European American University ta buƙaci shahararren mawaƙin Hausa, Dauda Kahutu Rarara, tare da sauran mutanen da aka ce an karrama a Abuja, da su tuntuɓe ta domin a tantance cancantarsu na samun digirin girmamawa na haƙiƙa.
A cewar wata sanarwa da jami’ar ta wallafa a shafinta na yanar gizo, idan aka tabbatar da cancantarsu, za a karrama su da digirin a hukumance a taron yaye ɗalibai da za a gudanar a Nijeriya cikin watan Nuwamba, 2025. Jami’ar ta kuma nanata cewa ba za a karɓi ko sisi daga wurin kowa ba, domin kaucewa ayyukan ƴan damfara.
- Digirin Bogi Aka Bai Wa Mawaƙi Rarara A Nijeriya – Jami’ar EAU
- Na Fi Ɗaukar Noma A Matsayin Sana’a Fiye Da Waƙa -Rarara
Haka zalika, jami’ar ta bayyana cewa ta riga ta fara bincike kan waɗanda suka shirya taron da aka gudanar a Abuja a matsayin karramawa, wanda ta bayyana a matsayin “Damfara” da aka yi ba tare da saninta ba.
DLC Hausa ta rawaito cewa, sanarwar ta biyo bayan nesanta kanta da taron da ya gudana a ranar Asabar, inda aka ce an bai wa Rarara da wasu mutane digirin girmamawa, abin da jami’ar ta ce ƙarya ne gaba ɗaya.