Wasu gungun ‘yanbindiga dauke da makamai, wadanda aka tabbatar da cewa masu garkuwa ne sun tafi da wani basarake, da ke garin Panyam mai suna Aminu Derwan, da ke karamar hukumar Mangu ta jihar Filato.
Majiyarmu ta shaida mana cewa, masu garkuwar sun yi wa fadar ruwan wuta kafin su tafi da basaraken.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar Filato, DSP Alabo Alfred, ya tabbatar da faruwar wannan lamari, wanda kuma ya ce, “Yanzu hakan nan da nake wannan magana, mun dukufa wajen gano inda aka kai wannan basarake domin mu kubutar da shi”
Kamar yadda DPO din da ke yankin ya fada cewa, sashin ‘yansanda masu yaki da masu garkuwa sun daura damarar ganin sun kubutar da wannan basarake.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp