Kimanin watanni biyu da barin ofis a matsayin mataimakin shugaban Nijeriya, Farfesa Yemi Osinbajo, ya samu mukami a fannin makamashi matakin duniya.
Osinbajo, wanda ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Talata, ya bayyana nadinsa a matsayin mai ba da shawara ga Global Energy Alliance for People and Planet (GEAPP).
- Osinbajo Da Tinubu Sun Yi Ganawar Sirri Kan Shirin Zaben 2023
- Osinbajo Bai Halarci Taron Yakin Neman Zaben APC A Filato Ba
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya kara da cewa ya ji dadin samun damar yin aiki a GEAPP.
Osinbajo ya rubuta cewa: “Ina matukar farin cikin sanar da cewa an nada ni mai ba da shawara ga Global Energy Alliance for People and Planet. Za mu yi aiki tare don buɗe hanyoyin samar da jari a fannin makamashi mai tsafta da kuma haɓaka kason Afirka a kasuwar carbon ta duniya. ta hanyar #ACMI
“GEAPP a cikin wannan dan kankanin lokaci sun nuna aniyar tallafa wa kasashe masu tasowa zuwa samar da makamashi mai tsafta ta hanyar amfani da nau’o’in da ke tabbatar da samar da makamashin duniya tare da samar da ci gaban tattalin arziki da samar da ayyukan yi don’t samun rayuwa mai dorewa da kuma cimma burin sauyin yanayi cikin gaggawa.
“Na yi farin ciki da samun damar yin aiki tare da @EnergyAlliance.”