Tsohon ministan harkokin Neja Delta, Godsday Orubebe, ya rattaba hannu kan rijistar zama mamban jam’iyyar APC a unguwar Tuomo da ke karamar hukumar Burutu ta jihar Delta.
Da yake jawabi a wajen taron wanda ya samu halartar ‘yan jam’iyyar, tsohon ministan ya gode wa shuwagabannin APC na kananan hukumomin da duk wadanda suka bar gidajensu da sana’o’insu daban-daban domin tarbarsa zuwa jam’iyyar.
- Malaman KASU Sun Janye Yajin Aiki Bayan Barazanar El-Rufa’iÂ
- Amurka Ta Kashe Shugaban Al-Qaeda A Wani Hari Da Ta Kai Afghanistan
Ya yi alkawarin yin aiki da dukkan ‘ya’yan jam’iyyar ba tare da nuna bambanci ba.
Orubebe wanda shi ne daraktan kungiyar yakin neman zaben dan takarar jam’iyyar APC a zaben gwamna na 2023, mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ovie Omo-Agege, ya shaida wa jam’iyyar cewa nan ba da dadewa ba za a shirya taron gangamin da ‘yan siyasa da dama daga wasu jam’iyyu da za su koma APC.
Ya kuma tabbatar wa APC cewa za ta ci zabe a karon farko a kananan hukumomin.
Ya kuma ce yana da yakinin cewa Omo-Agege ne zai lashe zaben gwamna kuma tabbas ci gaba zai zo yankin na Ijaw.
Da yake jawabi tun da farko, shugaban jam’iyyar APC a karamar hukumar, Mista Nana, ya ce shigar Orubebe abun al’ajabi ne ga jam’iyyar. Ya nemi hadin kan ‘ya’yan jam’iyyar a yanzu don tafiya tare.
Orubebe ya yi kaurin suna wajen adawa da Buhari da kuma gwamntinsa.
Ya shafe tsawon shekara takwas yana adawa da gwamnatin APC, amma daga karshe ya koma jam’iyyar.