Jami’an rundunar musamman na hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi (NDLEA) sun kama wani sanannen dillalin ƙwayoyi mai shekaru 60, mai suna Okpara Paul Chigozie, wanda ya kwashe shekaru bakwai yana guje wa hukuma, lokacin da yake ƙoƙarin aika miyagun ƙwayoyi zuwa Kudu maso Gabas da wasu yankunan Nijeriya.
An kama Okpara ne a maboyarsa da ke lamba 72, titin Michael Ojo, Isheri, Ojo, Jihar Legas a ranar Lahadi, 13 ga Yuli, 2025. A wancar safiyar da misalin ƙarfe 5:45 na safe, an cafke ɗaya daga cikin masu masa safara, Achebe Kenneth Nnamdi, mai shekaru 51, a Ilasamaja kan hanyar Apapa-Oshodi, a cikin motar Toyota Sienna.
- Matasa Sun Ƙona Ofishin NDLEA, Sun Kutsa Fadar Sarki A Kwara
- NDLEA Ta Cafke Masu Tura Alhazai Saudiyya Domin Safarar Hodar Iblis Zuwa Kasar
NDLEA ta ce, binciken da aka yi da Karnukan gano ƙwayoyi ya gano kilo 7.6 na hodar iblis da gram 900 na methamphetamine a cikin ɓangarorin jikin motar. Bayan haka, an kai samame a gidansa inda aka gano ƙarin kilo 1.8 na wata hodar iblis da kilo 1.3 na methamphetamine.
A filin jirgin sama na MMIA, Ikeja, jami’an NDLEA tare da ma’aikatan FAAN sun cafke wani fasinja mai shirin tafiya Italy da ƙwayoyin Tramadol da Rohypnol guda 7,790. A wani samamen kuma an kama Chioba Robert Uchenna da kwayar skunk 1.70kg da aka ɓoye a cikin abincin gwangwani da ake shirin tura wa Pakistan.
Haka nan, a wani otel mai ɗakuna 20 a Kosofe, Legas, jami’ai sun cafke Obayemi Oyetade da ƙwayoyi daban-daban ciki har da 1.3kg na alawar cakuletin wiwi da gram 900 na gummies. A Kaduna, an cafke mutum uku da kwayoyin skunk da Colorado da nauyinsu ya kai kilo 742.866.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp