Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sake buɗe cibiyar koyon tukin mota ta jihar Kano bayan shekara takwas tana a kulle. An kafa cibiyar ne a zamanin mulkin Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, amma ta bayan saukarsa sai aka kulle ta ba tare da amfani ba har zuwa yanzu.
A wajen bikin buɗe cibiyar, Gwamna Yusuf ya nuna damuwarsa kan yadda gwamnatin baya ta kasa kula da cibiyar, wanda hakan ya sa matasa suka rasa damar samun aiki da horon kiyaye haɗurran hanya.
- NCoS Ta Musanta Zargin Rashin Bai Wa Fursunoni Isasshen Abinci A Kano
- An Cafke Wani Hedimasta Bisa Laifin Sayar Da Kayayyakin Makaranta A Kano
A ranar farko da aka sake buɗe cibiyar, matasa 250 ne suka yi rajista. Gwamnan ya jaddada muhimmancin cibiyar wajen rage hatsari a kan hanya da kuma inganta sashen sufuri a jihar. Ya yi kira ga masu ruwa da tsaki a harkar sufuri su samar da ayyukan yi ga matasan da suka kammala wannan shirin horo.
Gwamna Yusuf ya kuma yi alkawarin samar da duk kayan da ake bukata don nasarar ci gaban cibiyar tare da ƙarfafa ɗaliban su rungumi horonsu da cikakkiyar himma.