Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta bayyana cewa martanin Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, game da sabuwar haɗakar ‘yan adawa ya nuna tsantsar fargabar faɗuwa mulki da ke damunsa da gwamnatin APC.
Mai magana da yawun sabuwar tafiyar jam’iyyun adawa, Malam Bolaji Abdullahi, ya ce a wata sanarwa ranar Alhamis cewa da gwamnatin Wike ta cika alƙawarinta ga ‘yan Nijeriya, da ba za a samu buƙatar kafa wannan gungu ba, kuma da Wike bai shiga ruɗani ba.
- Ƴan PDP Na Fice Wa Na Barin Jam’iyyar Ga Wike Da Ƴan Koransa – Dele Momodu
- David Mark Da Aregbesola Sun Zama Shugaba Da Sakataren Jam’iyyar ADC
Ya ce, “Idan da Wike ya biya albashin malamai da ke yajin aiki tsawon watanni a FCT, da bai raina ma’aikata ba, da bai yi biris da su don ya ci gaba da ƙaddamar da ayyukan da ba su da amfani ga talaka, ba zai ji tsoron wannan ƙungiya ba.”
Abdullahi ya ce ƙungiyar adawa na da hujjoji bisa yadda gwamnatin da Wike ke cikinta ta jefa talakawa cikin fatara da tsananin rayuwa. Ya ce suna cikin ɓacin rai da yadda yara ke kasa zuwa makaranta saboda malamansu ba su samun hakkokinsu, da yadda FCT ke fama da rashin tsaro. A cewarsa, babu yanda za a dakile wannan gungun ƴan adawa domin ya kasance mallakin ‘yan Najeriya da ke fatan ceto ƙasar daga kunci
n rayuwa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp