Jamhuriyar Nijar ta sanar da sabbin takunkumin bincike kan kayayyakin da aka shigo da su daga Nijeriya, bisa la’akari da karuwar matsalolin tsaro, in ji hukumomin Nijar.
Umarnin, wanda Kanar Mohamed Yacouba Siddo, Jami’in Hukumar Kwastam ya bayar, ya bukaci a sauke dukkan kayayyaki sannan a duba su sosai a iyakokin kasar da Nijeriya kafin a ba su izinin shiga Nijar.
- Tattalin Arzikin Sin Ya Gudana Bisa Daidaito Tare Da Samun Ci Gaba Da Juriya
- Sojoji Sun Kashe ‘Yan Bindiga, Sun Ceto ’Yan Kasuwa A Sakkwato
“Domin bukatun tsaro, dole ne a sauke dukkan kayayyakin da suka fito daga Nijeriya, sannan a duba su a ofisoshin shiga kafin samun izinin shiga kasar,” sanarwar ta kara da cewa kayayyakin da ke tare da takardu masu inganci daga tashoshin fitar da kayayyaki da aka amince da su, za a bincike su bayan sun isa inda aka yi nufin sauke su na karshe.
Kanar Siddo ya jaddada bin umarnin sosai kuma ya bukaci jami’ai da su bayar da rahoton duk wani kalubale yayin aiwatar da wannan doka.
Sanarwar ta zo ne jim kadan bayan da Burkina Faso ta tsare jami’an sojin Nijeriya 11 tare da kwace wani jirgin saman rundunar sojin saman Nijeriya bayan saukar gaggawa bayan jirgin ya shiga sararin samaniyar Burkinabe ba tare da izini ba.
ADVERTISEMENT














