A jiya Laraba 20 ga watan nan na Disamba, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya zanta da takwaransa na Philippine Enrique A. Manalo ta wayar tarho.
A gabar da alakar Sin da Philippines ta shiga wani yanayi mai sarkakiya, don gane da batun tekun kudancin Sin, tattaunawar da manyan jami’an biyu suka yi ta tarho, ta janyo hankulan sassan kasa da kasa. Yayin zantawar, bangaren Sin ya fayyace cewa, Philippines ta sauya matsayar ta, ta janye daga alkawuran da ta dauka, tana kuma ci gaba da takalar rigima a yankin teku, wanda hakan keta halastattun hakkokin Sin ne da moriyar ta bisa doka.
- Firaministan Sin Ya Jaddada Bukatar Kyautata Yanayin Kasuwanci Da Kara Habaka Kasuwanni
- Sin Ta Kara Tallafin Kudi Don Maido Da Wuraren Kiyaye Ruwa A Yankunan Da Girgizar Kasar Ta Shafa
Tun daga farkon wannan shekara, rahotanni na nuna yadda Philippines ta rika tura jiragen ruwan gwamnati, da na yaki, suna yin kutse a sassan ruwan dake daura da Ren’ai Jiao na tsibiran Nansha na kasar Sin, kana Philippines din ta rika aikewa da kayan gine gine zuwa ga jiragen dakon kaya na sojin ta da aka jibge ba bisa ka’ida ba, a wani mataki na wanzar da mamaya a yankin ruwan na Ren’ai Jiao.
Abun tambaya a nan shi ne, mene ne ya sa gwamnatin Philippine din aikata hakan? Masharhanta na ganin a daya bangaren, akwai murya mai karfi a Philippines dake ingiza batun tekun kudancin Sin, kuma shugaban Philippine na son amfani da hakan wajen karfafa karbuwarsa, ta hanyar nuna matsayin sa na rikau. A daya bangaren kuwa, yayin da hadin gwiwar Amurka da Philippines a fannin tsaro da sauran sassa ke kankama, manufofin waje na Philippines din sun fara karkara ga ra’ayoyin Amurka.
A fannin dangantakar Sin da Philippines, cikin shekarun baya bayan nan, Sin ta nuna halin dattaku, da hakuri wajen warware rashin fahimta game da batun tekun kudancin Sin tare da Philippines. To sai dai kuma hakan ba ya nuna cewa Sin za ta sadaukar da wani hakkin mulkin yankunan ta. Tun farkon wannan shekara ta bana, Sin ta rika daukar jerin hakikanin matakai na kare hakkokin ta.
Yayin tattaunawar manyan jami’an, bangaren Sin ya fayyace matsayarsa ga Philippine, wadda ta kuskurewa gaskiyar lamarin, ta yi gaban kan ta, har ma ta yi hadin kai da wasu sassa na waje, wadanda ba sa ga maciji da juna da Sin. Philippine ta ci gaba da aiwatar da matakan tada husuma, sai dai a na ta bangare, Sin za ta yi duk mai yiwuwa, wajen kare hakkokin ta kamar yadda doka ta tanada, tare da maida martani idan akwai bukatar hakan. Wannan wani gargadi ne a fayyace, wanda muke fatan zai sanya Philippines fahimta, da lura da halin da ake ciki, kana ta tsaya kan gaskiya a kalamanta da matakan da take aiwatarwa. (Mai fassara: Saminu Alhassan)