Kamfanin wayoyin hannu na Apple ya fitar da sabuwar wayar iPhone 14, wadda ke da manhajar da ke ba ka damar aika sakon gaggawa ba tare da internet ba, da kuma batir mai dadewa sosai fiye da na sauran wayoyin iPhone da aka fitar a baya.
An yi bikin kaddamar da iPhone 14 din ne a Amurka a hedikwatar kamfanin da ke Cupertino, inda a karon farko mutane sun halarci taron ido da ido tun bayan bullar annobar korona.
Apple ya fitar da kaloli hudu na iPhone 14, da kuma sabon agogon Apple Watch da kuma Airpod da ake makalawa a kunne.
Apple ya fitar da samfurin iPhone 14 ne girma biyu, wato iPhone 14 da kuma iPhone 14 Plus.
Waya ce da za ka iya samun damar neman agajin gaggawa ta amfani da tauraron dan adam a cikin dakika 15.
Haka kuma iPhone 14 din, tana da kyamara mai kyau wadda karfinta ya kai 12-megapidel, da ka iya daukar hoto mai kyau na wani abu yayin da yake motsi ko gudu.
Sannan kyamarar da ke daukar hoton selfie na da karfi da kyawon hoto fiye da ta iPhone din da ta gabace ta.
Kyamara na daga cikin abubuwan da kwastomomin iPhone ke bai wa muhimmanci, don a cewar Apple, masu amfani da iPhone sun cauki hoto tiriliyan uku a cikin shekara daya.
Kudin iPhone 14 na farawa ne daga dala 799 zuwa dala 999, ya danganta da girma da kuma samfurin da mutum yake so tsakanin iPhone 14 Pro ko kuma iPhone 14 Pro Mad. Wato Naira Miliyan 3,38,766.41 zuwa Naira Miliyan 4,23,564.01.
Ga mafi yawan masu amfani da wayar iPhone suna hada ta da na’urar makalawa a kunne ta Airpods. Sabbin da aka fitar na nemo inda dayan yake idan ya bata, ta hanyar yin tsuwa ko ‘yar kara kadan, wanda shi ma kudinsa ya kai dala 249. Wato Naira Miliyan 1,05,573.01.
Haka kuma akwatin da ake saka su na yin wata karar ta daban, idan aka danna manhajar da ke gano inda wayar iPhone take idan ana nemanta. Hakan na nufin za ka iya nemo Airpods dinka ta hanyar amfani da manhajar Find My iPhone da ke wayarka.
Sai kuma agogon Apple Watch Series 8 da kamfanin ya fitar, wanda ya zo da sabbin manhajoji da suka hada da wadda ke auna zafin jikin mutum, da kuma lokacin da mace kan iya daukar ciki bayan ta kammala al’ada.
Bugu da kari sabon Apple Watch na da manhajar da ke gano idan hatsarin mota ya auku, ta kuma kira lambar da za ta kawo maka agajin gaggawa nan take. Ga kuma batir da zai iya awa 36 idan aka cika shi.
Kudinsa na farawa ne daga dala 399. Wato Naira Miliyan 1,69,171.21.