Sabuwar jaruma a masana’antar finafinai ta Kannywood, ta bayyana shigowar ta masana’antar da cewa lokacin ta ne ya yi don haka ba ta yi mamaki ba da ta kasance cikin wadanda a ke damawa da su a cikin harkar, saboda yadda ta dade ta na son ta yi tun ta na karama don haka sai a yanzu ne ta samu cikar burin ta na zama ‘yar fim.
Jarumar ta bayyana hakan ne a lokacin tattaunawar mu da ita Inda take cewa, “Tsawon lokacin da na yi ina fatan na kasance ‘yar fim sai a yanzu na cika burina wanda a yanzu duk da ban dade da shigowa ba, don na fara ne a 2020 in da na fara fitowa a fim din ‘Hajiya Babba’ da ‘Ya’yan Mage’, kuma a yanzu ni ce jarumar fim din ‘Zo Mu Zauna’, kuma ina jin dadi sosai da hakan’.
Dangane da ko ta samu matsala daga gidan su a lokacin da ta shigo kuwa cewa ta yi, “Ai matsala sosai ma kuwa don har yanzu ina fuskantar matsalar, saboda ka san shi fim a nan kasar mu ta Hausa idan mutum ya na yi sai a rinka cewa shi dan iska ne.
To wannan ta sa har gida aka je a ke samun iyaye na ana cewa sun bar ni ina iskanci har abin ya yi musu yawa su ke ta mini magana, don haka sai nake fada musu cewa ni fa a rayuwa ta ba zan yi abin da bai dace ba, ni na san din sana’a ce kuma ita ta kawo ni, neman kudi nake yi, kuma ba wai zaman banza nake yi ba a Kano karatu nake yi sai kuma nake hadawa da fim saboda sana’a ce, don haka ba iskanci nake yi ba na dauke shi a matsayin sana’a da zan rinka yi ina rufawa kaina asiri, to haka dai suka yarda suka hakura tunda ya za su yi da ni, tunda ina cikin fim din na shiga dumu-dumu, kawai dai sai wani lokacin idan na je gida za a ce shikenan dai na shiga harkar fim ba zan yi aure ba.
Na Kano ce musu aure lokaci ne idan Allah ya kawo za a yi.”
Dangane da fim din da ta fito a matsayin Jaruma kuwa wato zo mu zauna cewa ta yi ‘Ina alfahari da fim din, domin shi ne ya fito da ni duniya ta san da ni kuma matsayin da aka ba ni na babbar Mace ya zo mini da bazata, saboda a matsayina na Budurwa da ban taba yin aure ba sai ga shi a fim na kasance matar aure har da babbar ‘ya da zan aurar da ita.
Wannan matsayin ya daga daraja ta sai na zo ina jin kaina kamar matar aure ka ga wannan ai daukaka ce, don haka a kullum ina alfahari da fim din ‘Zo Mu Zauna.”
A game da mu’amalarta da mutane kuwa cewa ta yi ta samu ce gaba sosai.”Domin duk lokacin da na je gida, sai ka ga duk wajen da na shiga a na ta zuwa wajena don ma ba ko’ina nake shiga ba saboda duk in da ka je za a ta kallon ka”.
A game da yadda mu’amalarta take kasancewa da masoyanta kuwa cewa ta yi abin ya na burge ta saboda “Duk in da na je a na zuwa a dauki hoto da ni kuma ina samun kyauta daga wajen masoyana sannan kuma idan na shiga cikin ‘yan fim mu kan zama kamar ‘yan’uwa don ba na gane ma ba a gida nake ba saboda an hadu an zama daya, haka a ke zama a yi wasa da dariya, don yau idan ba ni da lafiya na san wanda zan kira a cikin ‘yan fim ya tsaya a kaina.
Don haka muna zama ne kamar ‘yan uwan juna.”
Daga karshe ta yi kira ga jama’a da su daina yi wa ‘yan fim kallon ‘yan iska, saboda ba kowa ba ne dan iska, don akwai mutane nagari kamar kowacce harkar, da mutanen kirki da na banza, to haka ma harkar fim take. Inji Saratu Abubakar.