Shugaban kasar Nijar Mohmed Bazoum ya aika da sakon taya murna ga dan takarar jam’iyar APC Bola Ahmed Tinubu wanda hukumar INEC ta ayyana a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar Najeriya da aka gudanar a ranar 25 ga Fabrerun 2023.
A wasikar da sashen yada labaran fadar shugaban kasa ta aikawa manema Labarai, Shugaba Mohamed Bazoum ya ce “Ya kai dan uwana zababben shugaban Nijeriya Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, zaben da aka yi maka don shugabancin kasar Nijeriya ina yi maka barka ina kuma yi maka fatan alheri da samun nasarori a ayyukan da ke gabanka.
“Ina yi wa al’ummar Nijeriya jinjinar ban girma saboda jajircewarsu akan maganar tabbatar da dimokradiyya.
“A yadda aka yi zaben nan cikin yanayin mutunta ‘yanci da mutunta tsarin dimokradiyya da yanayin haske, abu ne da ke jaddada matsayin dimokradiyya a babbar kasarku, kuma alama ce da ke nuna ci gaban dimokradiya a nahiyar Afrika.” In nji Bazoum.
A karshen wannan wasika ta taya Bola Ahmed Tinubu murnar samun nasarar lashe zabe, shugaba Mohamed Bazoum ya ce “A madadina da al’ummar Nijar ina kara jinjina maka.”