Mahukuntan birnin Beijing fadar mulkin kasar Sin, sun sha alwashin inganta bincike, da amfani da fasahohin zamani don kyautata gabatar da abubuwa, da wuraren tarihi na birnin nan zuwa shekarar 2035.
Hukumar lura da kayayyakin tarihi ta birnin ce ta bayyana hakan, tana mai cewa shirin da aka yi domin cimma nasarar hakan, zai kunshi amfani da kirkirarriyar basira ko AI, da runbun manyan bayanai, da fasahar VR a gidajen adana kayan tarihi, da wuraren da ake killacewa tarihinsu.
Hukumar ta kara da cewa, za a kirkiri cikakken tsarin tattara bayanai na dijital mai kunshe a dukkanin kayan tarihi da ba a iya sauyawa wuri, ta hanyar amfani da bayanai daga jerin binciken da aka gudanar a matakin kasa na yanzu da wanda ya gabata. Kana za a yi amfani da sabbin abubuwa, da fasahohin kare tsaffin gine-ginen itatuwa daga lalacewa.
A daya bangaren kuma, za a yiwa gidajen baje kayayyakin tarihi babban garan bawul. Karkashin hakan, za a rika amfani da fasahar nuna bidiyo ta VR, domin baiwa masu ziyarar gidajen damar ganin abubuwan dake ajiye tamkar a gaske. Har ila yau, za a karfafa amfani da intanet, da AI domin inganta tsaron kayayyakin tarihi da tsarin kare su daga lalacewa. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp