Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, ta bayyana Lionel Messi da Karim Benzema da Kyalin Mbappe cikin ‘yan takarar gwarzon dan kwallon kafa na duniya na shekarar 2022 da ta gabata.
Idan za’a tuna Karim Benzema kan kwallo 15 da ya ci a Champions League da ta kai Real Madrid ta lashe kofin na 13 jumulla, sannan kuma tsohon dan kwallon tawagar Faransan shi ne kan gaba a yawan zura kwallaye a raga a La Liga a bana.
- Matsafa Sun Kashe Tare Da Cire Sassan Jikin Wani Dalibi A Adamawa
- Arewa An Sha Mu Mun Warke, Bai Kamata Mu Koma Gidan Jiya Ba –Matasan Arewa A Kudu
Shi kuwa Mbappe, wanda PSG ta lashe Ligue 1 a bara ya ci kwallo 26 a wasanni 46 da ya yi wa kungiyar Faransa sannan ya kuma taka rawar gani a gasar kofin duniya a Katar da lashe takalmin zinare da cin uku a wasan karshe da Argentina ta lashe kofin a bugun fenariti.
Messi kyaftin din Argentina ya taka rawar gani a Paris St Germain tun bayan da ya koma Faransa da buga wasa daga Barcelona a shekarar 2021 sannan ya bayar da gudunmuawar da PSG ta lashe Ligue 1 a kakar farko da ya buga mata wasa.
Har ila yau, shi ne ya ja ragamar Argentina ta lashe kofin, shi aka bai wa fitatcen dan wasa a babbar gasar kwallon kafa ta duniya ta shekarar 2022.
Za’a karrama fitatcen dan wasan kwallon na duniya a bana, kan rawar da ya taka tsakanin 8 ga Agustan 2021 zuwa 18 ga watan Disambar 2022.
Za dai a sanar da gwarzon dan kwallon kafa na duniya na FIFA a bikin da za’a gudanar ranar 27 ga watan Fabrairun nan da muke ciki na 2023 kamar yadda hukumar kwallon kafar ta FIFA ta tabbatar.
An tace ukun daga 14 da aka bayyana a baya, inda aka sa wasu kwararru suka tankade su zuwa ukun karshe da za a fid da gwani sannan za kuma a gudanar da zaben tsakanin masu koyarwa na tawagar mambobin FIFA da kyaftin-kyaftin da wasu ‘yan jarida da kuma kada kuri’a a intanet ta FIFA.