Shugaban kasar Amurka, Joe Biden, ya ce bai ga dalilin da zai sa Nijeriya ta rasa kujerar dindindin a kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya ba.
Biden, ya bayyana haka ne a lokacin tattaunawa ta wayar tarho da ya yi da shugaba Bola Tinubu.
- Sin Ta Yi Kira Da a Yi Hakuri Da Juna Tare Da Nuna Adawa Da Keta Zaman Lafiya a Yankin Gabas Ta Tsakiya
- Gwamna Abba Ya Amince Da Sabon Mafi Karancin Albashi Na ₦71,000 Ga Ma’aikatan Kano
Shugaban ya ce Amurka na kokarin ganin cewar nahiyar Afirka ta samu kujeru biyu a kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya.
A cewar ministan harkokin wajen Nijeriya, Yusuf Tuggar lokacin da yake tabbatar da tattaunawar shugabannin biyu, ya ce “Shugaba Biden ya nanata cewar bai ga dalilin da zai sa Nijeriya ba za ta samu daya daga cikin kujerun kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya ba, duba da irin matsayin kasar a nahiyar Afirka da muhimmancinta”
Tattaunawar shugabannin ta mayar da hankali kan alaka tsakanin kasashen biyu wajen tabbatar da bin doka da oda da kuma batun sakin shugaban kamfanin Binance da ke hada-hadar kudin crypto, Tigran Gambaryan.
Shugaba Tinubu ya gode wa shugaban Amurka kan hadin gwiwa da aiki tare a fannonin tsaro a nahiyar Afirka.