Shugaban kasar Amurka Joe Biden, ya bayyana tawagar kasar da za ta halarci rantsar da zabben shugaban kasa Asiwaju Bola Tinubu da za a yi a ranar 29 ga watan Mayun 2003.
An gayyato wasu shugabannin kasashen duniya, don halartar rantar da tsohon gwamnan Jihar Legas Tinubu a dadandalin Eagle Square da ke Abuja, inda Tinubu zai kasance shugaban kasa na 16.
- An Kwashe Wa Juventus Maki 10 A Gasar Seria A
- Kwana 6 Ga Rantsar Da Tinubu: ‘Yan Jarida Sun Yi Tsokaci Kan Yadda Aka Miƙa Mulki A Gwamnatocin Baya
Ana kuma sa ran tsoffin shugabanin kasa, jakadu da wakilan hukomomin gwamnati na kasa da kasa, za su halarci rantsuwar.
Biden, cikin sanarwar da fadar shugaban kasar Amurka ta wallafa a Intanet a daren jiya Litinin, ya sanar da sunayen tawagar Amurka ta mutum tara wadda sakataren Amurka na sashen gidaje da bunkasa birane Marcia L. Fudge zai jagoranta.
‘Yan tawagar na Amurka sun hada da, Mista David Greene, mai kula harkokin ofishin jakadancin Amurka a Nijeriya da ke Abuja, Hon. Sydney Kamlager-Dove, wakilin Amurka da ke a California, Hon Marisa Lago, sakataren harkokin kasuwanci na kasa da kasa, Janar Michael E. Langley, kwamandan Amurka na rundunar Amurka da ke aiki a Afrika, Hon Enoh T. Ebong, Daraktan hukumar sashen kasuwanci ta Amurka.
Sauran su ne, Hon Mary Catherine Phee, mataimakin sakataren Amurka na sashen harkokin Afrika, Hon Judd Devermont, mai taimaka wa shugaban kasa na musamman da kuma Hon Monde Muyangwa, mataimaki a sashen mulki na Amurka da ke aiki a Afrika.
A cikin shire-shiryen rantsar a rana 27 da watan Mayu, tsohon shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta, zai gabatar da kasida mai taken zurfafa demokiradiyya don a bunkasa.
Haka zalika, a ranar Alhamis, za a tabbatar wa Tinubu matsayin babban kwamandan tsaro na kasar nan GCON, inda kuma shugaban kasa mai barin Gado Muhammadu Buhari, zai karrama zababben mataimakin sa sanata Kashim Shettima, da lambar GCON.