Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano ta hana gwamnatin jihar Kano da jami’anta da ‘ƴansanda da Jami’an tsaron farin kaya da sauran hukumomin tsaron kama tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje.
Alkalin kotun, Mai shari’a A. M. Liman, a cikin takardar umarnin, mai dauke da kwanan wata 6 ga Yuli 2023 ya amsa wa masu shigar da korafin gaban lotus bukatarsu.
- Muhyi Ya Aike Wa Ganduje Sammaci Kan Bidiyon Dala
- Bincikenmu Ya Nuna Bidiyon Dalar Ganduje Gaskiya Ne –Muhyi
Umurnin ya ce: “Wadanda ake kara ko su da kansu ko kuma ta hanyar jami’ansu ko jami’an tsaronsu ko wani mutum ko gungun mutane da kar su kuskura su musguna ko tsoratarwa ko aikewa da wata barazanar kamawa ko tsare wanda ya shigar da korafi a gabanta.
Kotun ta ci gaba da bayar da Umarnin ko da wasa kar a kama daya daga cikin ‘Ya’ya ko wani daga cikin danginsa ko ma duk wanda aka nada wanda ya yi aiki a karkashin kulawar mai korafi ko duk wanda aka nada ko ya yi aiki a karkashin gwamnatin mai korafi har sai an yanke hukunci a kan neman dakatarwar.
Umarnin wucin gadi zai yi aiki har zuwa lokacin da za a saurari ƙorafin da aka shigar kan tauye ‘ƴancin ɗan adam zuwa ranar 14 ga Yuli, 2023.
Wadanda aka baiwa umarnin za a ba su kundin umarnin sa’o’i 36 daga ranar Juma’ar nan,” cewar Alkalin.