Shugaban Hukumar karbar korafe-korafe da yaki da rashawa ta Jihar Kano, Barista Muhyi Magaji Rimin Gado ya yi sammacin tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje domin amsa tambayoyi game da bidiyon Dala.
A 2017 ne jaridar Daily Nigerian, ta wallafa wasu jerin bidiyoyi da ke nuna Ganduje na cusa Dalar Amurka a aljihunsa.
- A Karon Farko Sanata Barau Ya Jagoranci Zaman Majalisar Dattawan Nijeriya
- Tinubu Ya Yi Garambawul Kan Dokokin Haraji
A cewar jaridar kudin cin hanci ne da gwamnan ke karba daga hannun ‘yan kwangila, amma Ganduje ya musanta.
Sai a ranar Laraba, Muhyi ya sanar da cewa binciken kwararru ya tabbatar da ingancin bidiyon.
Da safiyar Alhamis ne kuma ya ce ya aike wa Ganduje sammaci domin amsa tambayoyi gaban hukumar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp