Yayin da mabiya addinin Islama ke bikin babbar sallah, Shugaba kasa Bola Ahmed Tinubu ya roki al’ummar su ci gaba da hakuri da juriya, yana mai cewa wadannan su ne jigon babbar sadaukarwar da Annabi Ibrahim ya nuna.
“Babu wani aiki mafi girma da aka rubuta a tarihi fiye da misali mai kyau na Annabi Ibrahim wajen sadaukar da dansa daya tilo ga Allah,” in ji shugaban a wani sako mai taken: ‘Dole ne mu yawaita ayyukan alheri.
Shugaban ya kara da cewa yayin da muke nutsar da kanmu cikin farin ciki na wannan lokaci da murna, mu tuna wadanda suka mutu.
Shugaban ya ce yana sane da kalubalen tattalin arziki da kuma na tsaro da ke kara ta’azzara, ya tabbatar da cewa gwamnatinsa na kokarin sauke nauyin ‘yan kasa da samar da makoma mai kyau.
“Ina so in tabbatar muku cewa za a iya shawo kansu wannan lamari. Ina aiki dare da rana tare da tawagata domin samar da mafita. Mun fara ne da matakin da aka dauka zuwa yanzu don gyara tattalin arzikinmu da kawar da duk wani cikas ga ci gaban Nijeriya,” in ji Tinubu.
Wasu daga cikin gwamnonin sun bi sahun shugaban kasa wajen taya daukacin Musulmin da ke a fadin kasar nan murnan babbar sallah tare da kira na yin addu’o’in samun zaman lafiya da magance kalubalen rashin tsaro da kuma samun ci gaban jihohin baki daya.
Wakilinmu na Jihar Bauchi, Khalid Idris Doya ya ruwaito mana cewa, Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Muhammad ya taya al’ummar Musulmai musamman na jihar murna bisa bikin babbar sallar tare da jawo hankalinsu da su rungumi dabi’ar yafiya, son da kaunar juna, mutuntaka. Yayin da ya nemesu da su maida hankali wajen yi wa jihar addu’ar dorewar zaman lafiya da kwanciyar hankali domin ci gaba mai ma’ana.
Kazalika, ya kuma nemi al’ummar musulmai da su yi addu’a ta musamman domin samun damina mai albarka ta yadda za a samu cin gajiyar amfanin gona a wannan daminar ta bana.
“A yi hakan ba tare da la’akari da bambancin addini ko kabila, yare ko siyasa ba. Mu yi amfani da lokutan bikin babbar sallah wajen kyautata alaka da zamantakewarmu domin rayuwa mai inganci,” in ji gwamnan.
Gwamna Bala a sakonsa na barka da babbar sallar ga al’ummar jihar mai dauke da sanya hannun hadiminsa a bangaren yada labarai, Mukhar Muhammad Gidado a ranar Laraba, gwamnan ya ce, Alkur’ani mai girma ya koyar da dukkanin musulmai jin kai, kyautatawa, sadaukarwa domin neman lada a wajen Allah.
Gwamnan ya ce, akwai bukatar musulmai su yi amfani da lokacin sallar wajen waiwayen baya domin duba abubuwan da suka aiwatar a shekarar da ta gabata na kura-kurai domin duba hanyoyin gyara a wuraren da suke bukatar hakan wajen neman tsira a wurin Allah (SWT) a ranar gobe kiyama.
Da yake misalta addinin Musulunci a matsayin addinin da ke koyar da zaman lafiya da kwanciyar hankali tare da salama, ya tunatar da al’ummar musulman da su ci gaba da koyi da dabi’ar zama da kowa cikin kwanciyar hankali da lumana domin dorewar ci gaba.
Bala ya kuma nemi jama’an da su duba irin sadaukarwar da Annabi Ibrahim (AS) ya yi wajen sallama wa umarnin Allah da ya ce masa ya yanka dansa Annabi Ismail (AS), ya ce, hatta Layya da muke yi ya samo asali ne daga wannan sallamawar, don haka ne ya roki jama’an musulmai da su sallama lamarinsu ga Allah a kowani lokaci tare da bin umarninsa a cikin harkokin rayuwa.
A gefe guda ya ba da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da kokarin da ya dace wajen sauke nauyin da ke kanta tare da faranta wa al’umma da suka amince su sake zabinsa. Ya kuma ce gwamnatinsa za ta dukufa wajen ci gaba da shimfida ayyukan raya birane da karkara wanda kai tsaye za su taba rayuwar al’umma.
Ya nuna cewa halin da ake ciki na matsatsi lamari ne da ya shafi kasa baki daya, amma tuni gwamnatocin jihohi da na tarayya suka hada karfi da karfe wajen tunkuri matsalar, don haka ne yake ba da kwarin guiwar nan kusa za a samu saukin rayuwa.
Daga bisani gwamnan ya nemi addu’ar al’umma a kowani lokaci domin samun damar sauki nauyin da ke kansu, “Ina rokon jama’a da su kara hakuri kan lamarin da ake ciki zai wuce. A matsayinmu na gwamnati da muka san abun da ke kanmu, za mu ci gaba da nemi hanyoyin samar da tallafi da za su rage kaifin matsatsin rayuwa da ake ciki.”
A gefe daya kuwa, mataimakin gwamnan Jihar Bauchi, Honorabul Auwal Muhammad Jatau, ya bukaci al’ummar musulmai a jihar da su kara rungumar dabi’un zaman lafiya domin ci gaban da jihar ke kokarin samu ya kara habaka.
Jatau wanda yake taya mai gidansa, Gwamna Bala Muhammad da al’ummar jihar murna, tare da addu’ar Allah karbi ibadun bayinsa, ya ce lokacin babbar sallah lokaci ne na koyon sadaukarwa da sallamawa ga Allah (Madaukakin Sarki).
A sakon taya murna da sakataren watsa labarai na ofishin mataimakin gwamnan, Sani Muazu Ilelah, ya fitar, Jatau ya nemi musulmai da su yi la’akari da lokacin bikin sallar a matsayin na duba abubuwan da suka aiwatar a shekarar da ta gabata domin gyara kurakurai da suka yi don neman gafara a wajen Allah.
Jatau ya kuma yi kira ga jama’an jihar da su ci gaba da kasancewa masu gudanar da lamuransu cikin kwanciyar hankali a gabanin, lokacin, da bayan shagulan sallar domin dorewar rayuwa mai inganci a kasa da ma jihar.
Ya nemi jama’a da su jingine bambancin da ke tsakaninsu su dukufa wajen yin addu’ar dorewar zaman lafiya da kwanciyar hankali tare da rokon Allah ya kawo damina mai albarka.
Hakazalika, Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya taya al’ummar Musulmin jihar da ma na duniya baki daya murnar bikin babbar sallah ta bana, tare da yin kira a garesu da su rungumi dabi’ar sadaukarwa, biyayya da hakuri tare da yafiya ga juna.
A sakonsa na barka da sallah ga al’ummar jihar da ya fitar ta hannun Ismaila Uba Misilli, Babban Daraktan yada labarun Gwamnan Jihar Gombe, Gwamnan ya jaddada bukatar ci gaba da addu’o’i da karbar hukuncin Allah a kowane hali.
Ya kuma yi kira ga al’ummar Musulmin su ci gaba da addu’o’in samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a Jihar Gombe da kasa baki daya, musamman ma yanzu da aka samu sabuwar gwamnati.
Gwamna Yahaya wadda kuma shi ne Shugaban Kungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa, ya bukaci al’ummar Musulmin su yi amfani da wannar dama wajen kyautatawa da nuna kauna ga ‘yan’uwa da makwabtansu kamar yadda Annabi Ibrahim (AS) ya koyar kuma Annabi Muhammad (SAW) ya dabbaka.
Ya ce, “Yayin da muke bikin babbar sallar, ina kira a garemu, mu yi tunani da nazari kan sako da darusa wannan lokacin da ke koyar da cikakken biyayya, da sadaukarwa. Dole ne mu yi koyi da koyarwar Musulunci da ke karfafa zaman lafiya, hakuri da kauna.
“Ina kuma yi mana wasiyya da mu ci gaba da sadaukarwa don ci gaban jiha da kasarmu abar alfaharinmu, musamman a irin wannan muhimmin lokaci”.
Ya kuma yaba wa masarautun gargajiya da al’umma da malaman addini da daukacin al’ummar Jihar Gombe bisa goyon baya da fahimtar da suke yi wa gwamnatinsa tare da jaddada aniyar ci gaba da samar da shugabanci nagari da kuma karfafa nasarorin da aka samu kawo yanzu don kyautatuwar goben jihar.
Gwamnan ya kuma taya mahajjatan bana murnar gudanar da ayyukan ibada a kasa mai tsarki tare da addu’ar Allah Ta’ala ya karbi Ibadunmu baki daya.
A Jihar Zamfara kuwa, wakilinmu Hussaini Yero ya labarto mana cewa, gwamman jihar, Dauda Lawal ya yi kira ga al’ummar Jihar Zamfara da su kara hakuri a kan mawuyacin hali da suka tsinci kansu tare da yin addu’ar samun zaman lafiya a lokutan bukukuwan babbar sallah.
Dauda Lawal ya bayyana haka ne alokacin da yake gabatar da jawabin barka da babbar sallah a fadar gidan gwamnati da ke Gusau.
A jawabinsa ya bayyyana cewa, “Yau ba mu wuce wata guda ba da amsar mulki kuma gashi mun samu jihar cikin mawuyacin hali na rashin tsaro da ta barbarewar ilimi da matsalar ruwan sha da dai sauran kalubale da a yanzu haka muke fuskanta.
“Cikin taimakon Allah yanzu mun fara shawo kan matsalar ruwan sha na Gusau, kuma da yardar Allah sauran kananan hukumomi ma za mu san abun yi a kan su domin magance matsalar ruwan sha.”
Gwamna Dauda Lawal ya mika goron sallah ga Zamfarawa na albishir din magance matsalar da ake ciki da fatan za yi bukukuwan sallah lafiya.
A Jihar Kano kuwa, wakilinmu Abdullàhi Muhammad Sheka ya ruwaito mana cewa, gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf (Abba Gida-gida) ya taya al’ummar Jihar Kano murnar bikin babbar sallah.
Gwamnan ya ce, “Ya ‘yan’uwana jama’ar Jihar Kano, a madadina da gwamnatin Kano ina taya al’ummar Musulmi murnar zagayowar wannan rana mai albarka, ranar da al’ummar Musulmin duniya ke bikin babbar sallah. Haka Kuma muna addu’ar fatan alhazanmu da ke kasa mai tsarki suna gudanar da aikin hajjin wannan shekara, muna addu’ar Allah ya karbi ibadunsu, mu ma Allah ya karbi namu ibadun baki daya.
“Ya jama’ar Kano ina kara jadadda aniyar wannan gwamnati na kyautata harkokin lafiya, ilimi, samar da kyakkyawan yanayin gudanar da harkokin ciniki tare da inganta tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummar Jihar Kano baki daya, kyautata wa ma’aikatan gwamnati da ‘yan fansho tare da ci gaba da samar da abubuwan morewa rayuwa domin amfanin al’ummar Kano.
“Haka kuma muna godiya kwarai da gaske da hadin kai da goyon bayan da jama’a ke bai wa wannan gwamnati. A karshe muna kara kira ga jama’a da a yi kokari wajen gudanar bukukuwan sallah cikin nutsuwa da kiyaye doka da oda. Allah ya karbi ibadunmu ya kuma maimaita mana ta badin badada lafiya.”
Shi kuwa, gwamnan Jihar Neja Mohammed Umaru Bago ya yi kira ne ga Musulmi da su rungumi dabi’ar kaunar yin da’a kamar yadda kakanmu Annabi Ibrahim AS ya koyar da Musulmi.
Sakonsa wanda sakatarensa na yada labarai, Bologi Ibrahim ya fitar, gwamnan ya jaddada mahimmancin da babbar sallah take da shi, inda ya bukaci Musulmi da su yi amfani da damar ta sallah don kara karfafa imaninsu da mika al’amuransu ga Allah (SWA).
A nasa bangaren, gwamnan Jihar Filato, Barista Caleb Mutfwang ya yi kira ga Musulmai da su ci gaba da sadaukar da kawunansu wajen nuna kauna da son juna.
Mutfwang, a cikin sakonsa na murnar sallah wanda daraktansa na yada labarai Gyang Bere, ya fitar ta bai wa ‘yan jihar tabbacin cewa, gwamnatinsa za ta ja kowa a jiki.
Gwamnan Jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazak, ya ta ya Musulmi murnar bikin babbar sallah, inda ya ce, sallah na nuna yin imani ne da kuma mika wuya ga Allah (SWA).
A nasa sakon sallar, gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello ya bukaci ‘yan jihar da su rungumi dabi’ar kyautawa ga marasa karfi da kuma sadaukar da kai.
Sakon nasa wanda ya sa hannu da kansa ya shawarci Musulmi da su rungumi koyarwar da Annabi Muhammad SAW ya koyar.
Ita ma kungiyar kiristoci ta Nijeriya (CAN) ta yi kira ga daukacin ‘yan Nijeriya da su rungumi zaman lafiya, hadin kai da kaunar juna, tana mai jaddada cewa, Nijeriya za ta iya kaiwa ga kololuwar nasara idan ‘yan Nijeriya suka yi watsi da bambance-bambancen da ke tsakaninsu, suka hada kai don gina kasa mai daraja, hadin kai, da dimbin arziki.
Shugaban CAN, Archbishop Daniel Okoh ne ya yi wannan kiran a ranar Talata a sakonsa na barka da sallah domin taya al’ummar Musulmin Nijeriya murnar bikin babbar Sallah (Eid-el-Kabir).
A cewar shugaban kungiyar ta CAN, Hedikwatar kungiyar ta kiristoci ta bi sahun al’ummar musulmi wajen tunawa da kimar sadaukarwa, soyayya da biyayya da wannan rana ke wakilta.
“Muna sake yi wa ‘yan’uwa musulmi barka da sallah tare da addu’ar Allah Madaukakin Sarki ya ci gaba da bai wa al’ummarmu zaman lafiya da hadin kai da kuma wadata,” in ji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp