Mataimakin kwamishinan kula da harkokin zuba jari da kasuwanci na shiyya-shiyya, dake karamin ofishin jakadancin Najeriya da ke birnin Shanghai Hassan Mohammed, ya rataye takardun izinin shiga taruka da dama da ya taba halarta a ofishinsa. Daga cikinsu, takardun shiga bikin baje kolin hajojin da ake shigowa da su kasar Sin ko CIIE suna kan gaba.
Mohammed ya halarci dukkan bikin baje kolin CIIE guda 7 da aka gudanar a baya, kuma ya ganewa idonsa yadda ‘yan kasuwa masu sayar da dangin gyadar shazawa ko “cashew” daga Najeriya suka shigo kasuwar Sin ta hanyar baje kolin na CIIE.
A lokacin baje kolin da ya gabata, an ba da damar baje kolin dangin gyadar ta “cashew” daga Najeriya, matakin da ya haifar da karin kasuwanci tsakanin Sin da Najeriya a wannan bangare, ya kuma baiwa ‘yan kasuwa daga Najeriya damar shiga kasuwar Sin. Mohammed ya yi imanin cewa, baje kolin na CIIE ya bude hanya ga ‘yan kasuwar Najeriya ta samun nasarar kasuwanci. Ya ce “‘Yan kasuwa daga Najeriya sun kafa kamfanoni tare da ‘yan kasuwar kasar Sin, wanda hakan ya ba su damar fadada samar da kayayyaki, da habaka ayyukan yi a Najeriya, da kuma samun karin kudin shiga ga jama’a.”
Baya ga kasuwar Sin, Najeriya ta samu damar kulla hada-hadar kasuwanci da sauran sassa na duniya ta hanyar baje kolin na CIIE. Wani dan kasuwar Georgia, ya kulla yarjejeniyar ciniki da dan kasuwar Najeriya game da ridi a yayin taron na CIIE. Game da hakan, Mohammed ya bayyana cewa, kasancewar nisan da ke tsakanin kasashen biyu, idan ba don damar da CIIE ta samar ba, da wannan ciniki ya kasance mai wahala.
Yayin da ake daf da bude bikin baje koli na CIIE karo na 8, ana sa ran karin kayayyakin amfanin gona masu inganci daga Nijeriya za su shiga kasuwar Sin ta wannan dandali. Sin za ta ci gaba da bude kasuwanninta bisa nagartattun manufofinta ga duniya ta hanyar CIIE, tare da taka rawar gani wajen inganta hadin gwiwa da cin moriyar juna tsakanin kasa da kasa. (Mai Zane da Rubutu: MINA)
			




							








